Kolmani: Tinubu Ya Amince da Cigaba da Hako Man Fetur a Arewa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da lasisin aiki na dukkan matakan da ake buƙata don aiwatar da aikin haƙar mai a Kolmani
- Ministan albarkatun mai ya ce wannan matakin na da nufin ƙara yawan haƙar mai tare da amfani da dukkan damar da ake da ita
- Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya gode wa gwamnatin tarayya bisa wannan aiki, yana cewa zai amfani ƙasa baki ɗaya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da bayar da lasisin dukkan muhimman matakan da ake buƙata domin aiwatar da aikin man fetur na Kolmani da ke iyakar Bauchi da Gombe.
Ministan Albarkatun Mai, Sanata Heineken Lokpobiri, ya jagoranci kaddamar da ginin dindindin na makarantar Bauchi Oil and Gas Academy da ke ƙaramar hukumar Alkaleri a Bauchi.

Asali: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa a lokacin ne Sanata Heineken Lokpobiri ya bayyana umarnin da Bola Tinubu ya bayar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai ba Ministan shawara kan kafafen watsa labarai, Nneamaka Okafor ta ce cewa amincewar Tinubu na da nasaba da ƙudurin ƙara haƙar mai da farfaɗo da samar da albarkatun mai a ƙasar.
Dalilin cigaba da hako mai a yankin Arewa
Sanata Lokpobiri ya ce gwamnatin Tinubu na da nufin sauya fannin makamashi zuwa wani ɓangaren bunƙasa masana’antu, samar da ayyukan yi da ƙara kuɗin shiga.
Ministan ya yaba da yadda jihar Bauchi ke tafiya da manufofin gwamnatin tarayya ta fannin makamashi.
Lokpobiri ya bayyana kafa makarantar horar da ma’aikatan mai da iskar gas a jihar a matsayin muhimmin mataki na samar da ƙwararru.
Samar da masu aikin harkar mai a Bauchi
Ministan ya jaddada muhimmancin haɓaka ƙwarewar ma’aikatan cikin gida wajen tafiyar da albarkatun mai da iskar gas da Allah ya yi wa ƙasar Najeriya.
Ya yabawa PTDF bisa rawar da take takawa wajen horar da matasa da ƙwararru a ɓangaren makamashi, yana mai cewa ana sa ran sabuwar cibiyar za ta yi aiki tare da ita.
Bauchi na alfahari da hako mai a Kolmani
A nasa jawabin, Gwamna Bala Mohammed ya nuna godiyarsa ga gwamnatin tarayya bisa goyon bayan da ta ba wa aikin, yana mai cewa cibiyar horarwar za ta amfani Najeriya baki daya.
The Nation ta rahoto cewa Bala Mohammed ya ce:
“Ina tabbatar muku cewa wannan makaranta za ta zama wajen samun ƙwarewa ga matasan da za su amfanar da Najeriya baki ɗaya,”

Asali: Facebook
An fara aikin Kolamani ne Nuwamban 2022, wanda ke matsayin aikin haƙar mai na farko a Arewacin Najeriya.
NNPCL ta ce za a hako mai a Kolmani
A wani rahoton, kun ji cewa, shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari ya ce gwamnatin Bola Tinubu ba ta manta da hako mai a Kolmani ba.
A makon da ya gabata Bayo Ojulari, ya bayyana cewa kamfanin zai koma ci gaba da aikin haƙar mai a filin da aikin ke gudana.
Baya ga aikin hako man, shugaban kamfanin ya tabbatar da cewa akwai wasu muhimman ayyuka da suka shafi Arewa da za su yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng