Yawan Asarar da Aka Yi bayan Gobara Ta Laƙume Kwalejin Sheikh Dahiru Bauchi
- Gobara ta tashi a makarantar Sheikh Dahiru Bauchi da ke Bauchi, inda ta ƙone gini da kayayyaki masu yawa, ciki har da littattafai da kwamfutoci
- Daraktan makarantar ya ce lamarin ya faru ne bayan yamma, amma sun gode Allah ba a rasa rai ba ko jin rauni
- Hukumar kashe gobara ta ce an ƙone littattafai 7,228 da katifu da gadaje, yayin da ake ci gaba da bincike kan musabbabin gobarar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - An tafka asarar dukiyoyi da dama bayan tashin gobara a kwalejin Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Gobarar ta tashi a Kwalejin Alƙur’ani da Shehin malamin ya kafa a Rafin Albasa, Bauchi, inda ta ƙone ginin makarantar da kayanta.

Asali: Original
Gobara ta tashi a kwalejin Dahiru Bauchi
Binciken wakilin Aminiya ya nuna cewa wutar ta lalata ginin bene mai ɗakuna da dama ciki har da ofisoshi, ɗakunan karatu da kwamfuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rasa kayan dalibai da na malamai, ciki har da barguna, katifu, kayan amfanin yau da kullum da kuma kayayyakin makaranta.
Har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba a Sheikh Dahiru Bauchi kuma jami’an da abin ya shafa na ci gaba da bincike kan abin da ya haddasa lamarin.
Daraktan makarantar ya yi magana kan lamarin
Daraktan makarantar, Sayyadi Aliyu Sise Dahiru, ya ce suna godiya ga Ubangiji ganin cewa ba a samu asarar rai ba.
Ya ce:
"Muna gode wa Allah da babu wanda ya mutu ko ya ji rauni. Lamarin ya faru ne bayan an kammala karatu da yamma, kuma muna godiya ga jami’an kashe gobara."

Asali: Facebook
Bauchi: Gudunmawar da makarantar ke ba dalibai
Aliyu Sise bayyana cewa makarantar tana da alaƙa da Jami’ar Azhar ta ƙasar Masar, kuma Namadi Sambo ne ya ƙaddamar da ita.
Makarantar na koyar da ilimin Islamiyya da na boko kuma kowace shekara ana yaye mahaddatan Alƙur’ani.
Majiyoyi suka ce ɗalibai da dama suna samun horo ta ɓangarori da dama kama daga sana'o'in hannu na rayuwar yau da kullum da kuma tarbiyyar addinin Musulunci.
“An rasa litattafan Sheikh Dahiru Bauchi da na malamai da kwamfutoci da wasu muhimman kayan makaranta."
- Cewar Daraktan
Yawan asarar da aka yi sanadin gobarar
Hukumar kashe gobara ta Bauchi ta ce gobarar ta ƙone littattafai 7,228, kayan ɗalibai 583, darduma, kujeru da takardu 150.
Jami’an gwamnati na ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainahin musabbabin gobarar da ta tashi a makarantar da kuma neman hanyar daƙile faruwar haka a nan gaba.
Gwamna Bala ya kaddamar da makarantar Dahiru Bauchi
A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar da makarantar tunawa da Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ake ganin ita ce irinta ta farko a Arewa maso Gabas.
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya ce za a gina irin makarantar a kowanne daga cikin kananan hukumomi 20 na jihar.
Makarantar za ta magance matsalar yara marasa zuwa makaranta tare da samar da yanayi mai kyau domin karatu ga yara da malamai.
Asali: Legit.ng