Samfurin danyen man fetur da aka tona a rijiyar man Kolmani ya fito

Samfurin danyen man fetur da aka tona a rijiyar man Kolmani ya fito

  • A yau ne 22 ga watan Nuwamba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da mahakar mai ta farko a Arewa
  • Hadimin shugaban kasa ya nuna kalan man da aka hako a mahakar man, lamarin da ya jawo cece-kuce a Twitter
  • 'Yan yankin Kudu da Arewa na can Twitter suna tafka cece-kuce tun bayan da aka kaddamar da aikin mai na Kolmani

Arewa maso Gabas - An yada wasu hotuna guda biyu da ke nuna samfurin danyen man fetur da aka hago da rijiyar mai ta farko da aka tona a Arewacin Najeriya, lamarin da yasa aka kaure da cece-kuce a Twitter

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai ne ya yada hotunan a shafinsa na Twitter a ranar Talata 22 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Buhari ya kaddamar da mahakar man fetur ta farko a jihohin Arewacin Najeriya

A cewarsa, an hako danyen man ne daga sabuwar rijiyar mai ta Kolmani da ke tsakanin jihohin Gombe da Bauchi a Arewa maso Gabashin Najeriya.

An kaure a Twitter kan batun samo man fetur a Arewacin Najeriya
Samfurin danyen man fetur da aka tona a rijiyar man Kolmani ya fito | Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

A kalamansa, cewa ya yi:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Samfurin danyen mai daga mahakar man Kolmani, da ke jihohin Gombe da Bauchi."

A tun farko, gwamnatin Buhari ta fara aikin mahakar man Kolmani shekaru da suka gabata, sai yanzu aka samu nasarar kammala aikin, kuma a yau Talata ne shugaba Buhari ya kaddamar da rijiyoyin da aka tona.

'Yan yankin Kudu na ta cece-kuce kan fara hako mai a Arewa

A kasan rubutun Bashir Ahmad, jama'a da dama sun yi martani, inda wasu daga yankunan Kudancin kasar nan ke nuna alamar adawa da wannan ci gaba da kasar ta samu.

A banagre guda, wasu 'yan Arewa sun bayyana shakku kan tabbacin wannan aiki, duba da abubuwan da ke faruwa a kasar.

Kara karanta wannan

Yayinda Buhari Ke Shirin Kaddamar Da Aikin Hako Mai A Bauchi, Jama'ar Alkaleri Sun Gabatar da Bukatunsu

Ga dai kadan daga martanin jama'a:

@MichaelOrbiam yace:

"Ina da yakinin cewa, wannan man daga Neja Delta aka sato shi kuma an ajiye shi ne don kawai a yi mana bulayin cewa Arewa ka samu danyen man fetur."

@EemmanuelMadu yace:

"Kalli yadda kake jin dadi, amma ga can wasu yankuna a kasar nan da jihohinsu ke baku arziki amma baku taba nuna yaba musu ba."

@kassimisola yace:

"Abu ne mai kyau, shikenan ku ma sai ku fara tsaya da kafafunku akan mai yanzu. Kawai kowa ya kama gabansa..."

@MikanoLeader yace:

"Kenan yanzu gwamnonin Arewa maso Gabas za su fara karban 13% daga gwamnatin tarayya na jihohin da ke samar da man fetur
"Bash ina fatan dai kada ya zama irin aikin Mambila fa."

@imustaphaa yace:

"Gani dai abin yarda ne. Ganin haka yana da kyau. Allah ya yiwa Buhari da tawagarsa albarka."

Kafin nan, an fara samun sabani tsakanin jihohin Gombe da Bauchi kan wace jiha ce ainihin mai mallakar wannan mahakar mai da aka samo.

Kara karanta wannan

Alkawuran Atiku: Zan yiwa Arewa aiki kamar Abubakar Tafawa Balewa idan na gaji Buhari a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel