Abin Tausayi: An Rasa Rayuka, Mutane 21 Sun Jikkata yayin Rabon Kuɗi a Borno

Abin Tausayi: An Rasa Rayuka, Mutane 21 Sun Jikkata yayin Rabon Kuɗi a Borno

  • An tabbatar da mutuwar mutum uku yayin da wasu 21 suka jikkata a cunkoson da ya faru a garin Bama a Borno yayin rabon kudin tallafi
  • Shaidu sun ce cunkoson ya faru ne a makarantar firamare ta Kasugula inda jama’a suka taru domin karɓar N28,500 daga ICRC da UNICEF
  • An kai waɗanda suka jikkata asibiti, amma wasu biyu sun rasu daga baya, gwamnati ta kuma tura jami’ai don kwantar da tarzoma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bama, Borno - An shiga tashin hankali a garin Bama da ke jihar Borno bayan turmutsutsu da aka samu na jama'a yayin rabon kudin tallafi daga hukumomi.

An tabbatar cewa mutane uku sun mutu sannan da dama suka jikkata sakamakon cunkoso a wajen rabon kudin agaji saboda halin da ake ciki.

An rasa rayuka a Borno kan rabon kudi
Mutane 3 sun mutu a Borno saboda rabon kudi. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Facebook

Rabon kuɗi ya yi sanadin rayuka a Borno

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa hukumomin ICRC da UNICEF ne suka shirya rabon kudin a Bama da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidu sun bayyana cewa cunkoson ya faru ne a ranar 15 ga Mayu da misalin ƙarfe 8:00 na safe a makarantar firamare ta Kasugula.

Wannan makaranta na daya daga cikin wuraren da aka ware domin rabon kudin N28,500 ga mabukata a garin Bama.

Lamarin ya rikice ne bayan mutane sun fara turmutsitsi zuwa ƙofar makarantar wanda ya haddasa cunkoso mai muni da ya jawo asarar rayuka.

Jerin waɗanda abin ya shafa a Borno

Waɗanda suka jikkata sun haɗa da Falmata Alhaji Modu, Falmata Modu, Tella Babagana Tujani, da Bulama Yakime, duk ’yan garin Bama.

Sauran sun haɗa da Amina Mohammed, Mallam Akura, Fatima Bukar, Yagana Ibrahim, Fatima Mohammed, da Fatima Abatcha da Zara Lawan.

Haka kuma Inde Modu da Aisha Abdullahi sun jikkata yayin cunkoson da aka samu wanda ya tayar da hankulan al'ummar yankin.

Sannan an tabbatar da cewa Bukar Labddo mai shekara 60 daga unguwar Bukar Tela ya rasu a asibiti nan take.

Wasu sun mutu yayin rabon kudi a Borno
Mutum 3 sun mutu wasu 21 sun jikkata a Borno. Hoto: Legit.
Asali: Original

Borno: Matakin da jami'an tsaro suka ɗauka

Hukumomin asibitin suka ce wasu biyu daga cikin waɗanda suka jikkata sun rasu yayin da ake basu kulawa a asibitin Bama.

Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaro sun garzaya wurin don daidaita al’amura da kuma kai marasa lafiya zuwa asibiti.

An mika gawar mamatan ga iyalinsu domin a yi musu jana’iza bisa ga tsarin addinin Musulunci ba tare da bata wani lokaci ba.

Legit Hausa ta tattauna da masanin tattalin arziki

Lamido Muhammad Bello ya koka kan yadda talauci ke kara tunzura al'umma hallaka kansu wurin neman tallafi.

Ya ce:

"Babu wani amfani ko rage radadin halin kunci da rabon kudi ko tallafi ke yi, ya kamata a samar da sana'o'i da abubuwan more rayuwa ga al'umma."

Bello ya ce har yanzu yan Najeriya ba su dauko hanyar koyawa yan siyasa darasi duk da jefa su a mummunan yanayin da suka yi.

An rasa rai yayin cunkoso a filin Idi

Kun ji cewa rundunar ‘yan sandan Gombe ta tabbatar da mutuwar yara biyu sakamakon turmutsutsu da ya auku a babban filin Sallar idi na Gombe.

An ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:45 na safe yayin da jama’a suka yi kokarin fita cikin gaggawa, lamarin da ya janyo jikkatar mutum 22.

An garzaya da wadanda suka jikkata asibitoci daban-daban, yayin da Gwamna Inuwa Yahaya ya dauki nauyin jinyar dukan wadanda suka samu raunuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.