Zargin Fargabar Mutuwa Ya Jawo Karyewar Farashin Shinkafa Warwas
- Farashin buhun shinkafa kilo 50 ya fadi zuwa N54,000 sakamakon jita-jitar shinkafa na kashe mutane da kuma yawan shigo da ita kasa
- Mutane da dama sun guji siyan shinkafa bayan samun saƙonni a WhatsApp da ke cewa an mutu a Badagry da Idiroko a Lagos
- Duk da musun jami’an kwastam da ‘yan kasuwa, rahoton S&P Global ya tabbatar da cewa yawan kaya da ƙarancin bukata ne ke jawo saukar farashin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Farashin buhun shinkafa mai kilo 50 ya fadi zuwa N54,000 bayan jita-jitar cewa akwai shinkafa mai kashe mutane a kasuwa.
Ana cewa farashin ya sauka daga N58,000 a watan Afrilu bayan buƙatar shinkafa ta ragu saboda rade-radin mutuwa a Badagry da Idiroko da ke Lagos.

Asali: Getty Images
Farashin shinkafa ya fadi kan fargabar mutuwa
Buƙatar shinkafa ta ragu kwanan nan yayin da iyaye da ‘yan uwa ke aikawa da saƙonni, suna gargaɗi ka da a sayi ko a ci shinkafar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce wani yana yada saƙon WhatsApp da cewa sama da mutane 70 sun mutu kwanakin baya bayan cin irin wannan shinkafar.
Duk da Hukumar Kwastam ta Najeriya a Seme ta karyata jita-jitar, an lura da cewa masu amfani sun daina siyan shinkafa, hakan ya sa farashi ya ragu.
Majiyoyi sun tattaro cewa buhun shinkafa mai kilo 50 yanzu ya kai N50,000 a wuraren da ke kusa da iyakoki.
‘Yan kasuwa a Badagry, saboda rashin ciniki, sun fitar da bidiyo a Alhamis da Juma’a, suna karyata jita-jitar shinkafa mai kisa.
Masu sayar da shinkafa sun ce jita-jitar ba gaskiya ba ce kuma babu wanda ya mutu sakamakon siyan ko cin shinkafa.

Asali: Original
Dalilin karuwar faduwar farashin shinkafa
Rahoton farashin shinkafa na baya-bayan nan daga S&P Global ya nuna cewa farashin shinkafar na Yammacin Afirka ya fadi sosai.
S&P Global ta ce hakan na faruwa ne sakamakon ƙarancin buƙata da kuma yawan kaya da aka shigo da su yankin.
Masu shigo da kaya a Benin sun nuna damuwa kan faduwar farashin, suna danganta hakan da yawan shinkafar daga India.
Rahoton ya ce:
“Matsalar yawan kaya ba a Benin kaɗai take ba. A Togo, ma su shigo da kaya na fuskantar irin haka.”
Wani ɗan kasuwa ya ce farashin jigilar kwantaina da buɗaɗɗun kaya ya ragu zuwa $3-$4 kan kowace metric ton.
An ce Benin ce ta fi shigo da shinkafa daga India, sannan Guinea da Ivory Coast suka biyo baya.
BUA ya magantu kan faduwar farashin abinci
Kun ji cewa shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya ce za su ci gaba da rage farashin shinkafa, sakamakon sauƙin haraji daga gwamnati.
Attajirin ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa dakatar da harajin kwastam a 2024, yana mai cewa hakan ya rage tsadar shinkafa da masara sosai.
Abdul Samad ya bayyana yadda masu adana shinkafa ke haddasa hauhawar farashi, amma ya yi alkawarin ci gaba da karya fashin abinci.
Asali: Legit.ng