"Rabon Kudi bai Tabuka Komai ba," Bankin Duniya Ya Soki Tsarin Tinubu da Buhari

"Rabon Kudi bai Tabuka Komai ba," Bankin Duniya Ya Soki Tsarin Tinubu da Buhari

  • Babban Bankin Duniya (WB) ya bayyana shirin raba tallafi na musamman na N5000 ga talakawan kasar nan bai yi amfanin komai ba
  • Wannan na kunshe cikin rahoton da babban bankin kasar nan CBN ya fitar mai taken “tasirin raba tallafin kudi ga mata da gidaje a Najeriya
  • Bankin duniya ya bayyana cewa babu wasu alkaluma da suka tabbatar da ikirarin gwamnatin tarayya na cewa an samu nasara sosai wajen raba tallafin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Babban Bankin Duniya (WB) ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na raba tallafi na musamman na N5000 ga talakawan kasar nan da bai yi amfanin komai wajen habaka tattalin arzikin mutanen ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: "'Yan adawa na gagarumin shirin kifar da gwamnatin APC", Utomi

Wannan na kunshe cikin rahoton da babban bankin kasar nan CBN ya fitar mai taken “tasirin raba tallafin kudi ga mata da gidaje a Najeriya.”

Bankin Duniya
Bankin Duniya ya ce shirin raba tallafin gwamnatin tarayya bai yi amfani ba Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

A rahoton da Channels Television ta wallafa, shirin bai yi wani tasiri wajen rage rashin aikin yi musamman tsakanin mata a kasar nan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Raba tallafin bai yi amfani ba,” Rahoto

Gwamnatin tarayya ta cikin rahoton da babban bankin kasa CBN ya fitar ya bayyana cewa shirin raba tallafin N5000 ga talakawa ya cicciba tattalin arzikin masu karamin karfi.

“Mun gano an samu ci gaba ga masu kula da gidajensu, sun kara samun farin ciki, iya daukar matakai wajen kashe kudinsu, da kuma ‘yancin zirga-zirga,” cewar rahoton.

Sai dai bankin duniya ya bayyana cewa babu wasu alkaluma da za su tabbatar da sahihancin nasarar da gwamnatin ke ikirarin an samu, kamar yadda The Cable ta wallafa.

Kara karanta wannan

"Yana da kyau amma...": Dattawan Arewa sun bayyana matsayarsu kan harajin CBN

Gwamnati ta fara raba tallafi

A baya mun kawo muku cewa gwamnatin tarayya za ta fara raba tallafin N50, 000 ga masu karamin karfi ta shirin bayar da tallafi mai dauke da sharadi na shugaban kasa (PCGS).

Ministar kasuwanci, Doris Aniete ce ta bayyana hakan a sakon da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce za a bawa wasu ‘yan Najeriya da ake tantance nasu tallafin kudin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel