Kalaman da Suka Jawo Pantami Ya Yi wa PDP Muguwar Addu'a a 2012

Kalaman da Suka Jawo Pantami Ya Yi wa PDP Muguwar Addu'a a 2012

  • Ana cigaba da tattaunawa kan addu'ar da Sheikh Isa Ali Pantami ya yi a kan jam'iyyar PDP a lokacin Goodluck Jonathan kan rashin tsaro
  • Maganganu sun yawaita ne bayan tsohon ministan sadarwan ya koma jam'iyyar PDP domin tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe
  • A 2012, tsohon mai ma shugaba Jonathan shawara kan tsaro, Andrew Azazi ya alakanta PDP da Boko Haram, lamarin da ya fusata Pantami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - A kwanakin baya, Sheikh Isa Ali Pantami ya kawo dalilan kan yi wa jam'iyyar PDP mummunar addu'a saboda rashin tsaro.

Ya ce ya yi haka ne saboda abin da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro na wancan lokacin, Andrew Azazi ya fada kan Boko Haram.

Kara karanta wannan

Fasto ya taro rigima da Sheikh Jingir kan APC ta ba Musulmi takara a Jos

Sheikh Isa Ali Pantami
Wani lokaci da Sheikh Isa Ali Pantami ke wa'azi a Abuja. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Twitter

Me Andrew Azazi ya fada?

Rahoton Channels TV ya nuna cewa tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Andrew Owoye Azazi, ya daura karuwar hare-haren kungiyar Boko Haram kan rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar PDP a 2012.

Janar din mai ritaya ya bayyana hakan ne a rana ta biyu ta taron bunkasa tattalin arzikin yankin Kudu maso Kudu, inda aka tattauna matsalar tsaro da ta dabaibaye Najeriya a wancan lokacin.

Yayin da yake bayani kan yadda hare-haren Boko Haram suka karu, Azazi ya ce:

“Ba a samu irin wannan yawaitar tashin hankali a Najeriya ba sai lokacin da shugaban kasa na yanzu ya bayyana cewa zai tsaya takara.”
“PDP ta yi kuskure tun daga farko, tun daga lokacin da ta ce mutum kaza zai iya mulki, wani kuma ba zai iya mulki ba… bisa dokoki da ka’idojin PDP ba bisa kundin tsarin mulkin kasa ba, kuma hakan ya haifar da yanayin da ya kai ga abin da ya bayyana yanzu.”

Kara karanta wannan

"Ni ma na rame": Tinubu ya amince manufofinsa sun jefa ƴan Najeriya a wahala

Ya kuma bayyana cewa hare-haren bama-bamai, hare-haren kunar bakin wake da karya gidajen yari da suka addabi Arewacin kasar:

“Ana iya danganta su da siyasar wariya da PDP ta yi a yankin.”
Andrew Owoye Azazi
Tsohon NSA, Andrew Owoye Azazi. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Martanin Jonathan kan kalaman Azazi

Shugaba Goodluck Jonathan ya nuna mamaki kan kalaman da Andrew Azazi ya yi a taron tattalin arzikin yankin Kudu maso Kudu, inda ya ce tsarin rabon mulki na jam’iyyar PDP ne ya haddasa matsalar tsaro a kasar.

Daily Trust ta rahoto tsohon shugaban kasar ya ce:

“Na karanta a wasu jaridu inda wasu ‘yan jarida suka rawaito abin da aka ce mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya fada.
"Har sai na karanta rahotonsa da kuma sauraron abin da ya fada da kansa, ban san abin da zan yi ba. A matsayinmu na mutane, muna iya sabani domin cimma matsaya.
"Shi ya sa masu rike da mukaman siyasa irinmu dole su yi taka-tsantsan wajen abin da suke fada, domin mutane na iya kallonsa ta wata fuska dabam.

Kara karanta wannan

"Ba dan koyo ba"; Atiku ya gano dan takarar da ya cancanci tutar ADC don karawa da Tinubu 2027

"Amma kamar yadda na fada, har sai na saurare shi da kaina, ban yarda cewa yana nufin rikicin neman mulki a PDP ne ke haddasa rashin tsaro a kasar ba.”

Pantami zai yi takara a PDP

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya koma jam'iyyar PDP kuma ta tsayar da shi a matsayin wanda zai mata takara a 2027.

Sheikh Isa Ali Pantami ya koma PDP ne bayan ya kaddamar da kudurin neman gwamna a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya a kwanakin baya.

Wasu daga cikin masu neman takara sun nuna kin amincewa da tsayar da Pantami, inda suka ce ba a yi masu adalci ba kwata-kwata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng