An Kashe Shanu Sama da 100 a Sabon Harin Filato, Fulani Sun Fadi wanda Suke Zargi
- Rahotanni na nuni da cewa wani sabon hari da aka kai wa makiyaya a Filato ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya da fiye da shanu 100
- Kungiyar MACBAN ta bayyana cewa matasan Berom daga wasu kauyuka ne suka kai harin, suka kashe dabbobin, sannan suka yanka wasu
- A yayin da Fulani ke kira da a kawo karshen hare-haren da suke cewa ana kai musu ba tare da dalili ba, matasan Berom sun musanta zargin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - An sake samun sabon rikici tsakanin makiyaya da wasu matasa a jihar Filato, lamarin da ya yi sanadin rasa rai da asarar dabbobi masu yawa a Jos ta Arewa da ta Kudu.
Harin ya zo ne a cikin makonni biyu da ake fuskantar kai hare-hare a kan makiyaya da sace musu dabbobi, kamar yadda kungiyar Miyetti Allah ta tabbatar.

Asali: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa MACBAN ta ce an kai harin ne ranar Talata da Laraba a kauyukan Gero da Darwat, aka kashe fiye da shanu 100 da makiyayi guda da jikkata wasu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
MACBAN ta zargi Berom da kashe shanu
Sakataren MACBAN na jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo ya bayyana cewa matasan Berom daga yankin Gero ne suka kai harin a ranar 13 ga Mayu, suka kashe fiye da shanu 70.
Ya ce:
"Sun yanka wasu daga cikin shanun, suka dauki naman. Rundunar Operation Safe Haven ta kama mutum uku dauke da naman dabbobin da aka kashe.”
A cewar Babayo, hari na gaba ya faru ne a Darwat a ranar Laraba, aka sake kashe fiye da shanu 40, kuma an sace namansu.
Halin da aka shiga bayan kashe shanu a Filato
Daya daga cikin wadanda aka kai wa hari, Shagari Ibrahim ya bayyana cewa lamarin ya jefa su cikin firgici, inda aka zo da makamai aka fara harbin dabbobi ba kakkautawa.
Daily Post ta rahoto Shagari Ibrahim ya ce:
"Mun rasa komai. Dabbobinmu sun mutu ba tare da wani laifi ba. Muna kira ga gwamnati da ta dauki mataki domin hana sake faruwar hakan.”
Wani da abin ya shafa mai suna Musa Ibrahim ya ce sun ga matasa sun nufo su da makamai daga bangarori daban-daban, inda suka fara harbin dabbobin ba tare da wata takaddama ba.
'Yan Berom sun musanta zargin kashe shanu
Shugaban kungiyar matasan Berom, BYM, ya ce ba su da masaniya kan harin da aka kai, yana mai kiran zargin da MACBAN ta yi a matsayin karya da kage.
Ya kara da cewa mutanensu masu bin doka ne kuma ba su da hannu a cikin irin wadannan ayyuka na rashin tausayi da ake zarginsu da aikatawa.

Asali: Getty Images
Kashe shanu: Gwamnatin Filato za ta yi bincike
Kwamishinar yada labarai ta jihar Filato, Joyce Ramnap, ta ce har yanzu ba ta samu cikakken bayani kan lamarin ba, amma ta yi yunkurin tuntubar shugaban karamar hukumar Riyom.
Joyce Ramnap ta ce za a gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar abin da ke faruwa a yankunan.
Rikicin makiyaya da manoma
Rikicin manoma da makiyaya na ci gaba da haifar da mummunan tasiri ga ci gaban jihar Filato.
Duk lokacin da aka samu sabani tsakanin wadannan rukuni biyu, abin yana janyo hasarar rayuka, dukiyoyi da kuma tabarbarewar tattalin arzikin yankunan karkara.
Rikice-rikicen sun hana mutane yin noma da kiwo cikin kwanciyar hankali, lamarin da ke kara yawan yunwa da hauhawar farashin kayan abinci.
Manoma na jin tsoron shiga gonaki, yayin da makiyaya ke fuskantar fargaba na rasa dabbobinsu ko samun hare-hare.
Hakanan, rikicin yana haddasa karancin abinci a kasuwanni, yana kara jefa talakawa cikin mawuyacin hali.
Yara na barin makaranta saboda matsin tattalin arziki, mata na rasa ‘yan uwansu ko mijinsu da ke rike da nauyin iyali.
Har ila yau, ci gaba da tashin hankali na hana zuwan masu zuba jari da kuma gina sabbin ayyukan raya kasa a yankunan da ake fama da rikici.
Saboda haka, sai gwamnati da shugabannin gargajiya da na addini su hada kai wajen nemo hanyar da za a shawo kan wannan rikici da dadewa.
An kai hari kasuwa a jihar Filato
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai mummunan hari wata kasuwa a jihar Filato.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kai hari a wani gari a karamar hukumar Wase kafin shiga kasuwar.
Wani mai sayar da kaya a kasuwar ya ce 'yan bindigar sun bude wuta ga 'yan kasuwa yayin da suka shiga kasuwar, kuma sun yi sata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng