Iyalan Mafarutan Kano da aka Babbake a Uromi Sun Ji Shiru, Sun Yi Zanga Zanga

Iyalan Mafarutan Kano da aka Babbake a Uromi Sun Ji Shiru, Sun Yi Zanga Zanga

  • Iyalan mafarautan da aka kashe a Edo sun gudanar da addu’a da zanga-zangar lumana a Kibiya aKano, kwanaki 40 bayan kisan yan uwansu
  • Sun koka da rashin sahihin bayani daga gwamnati, inda suka bukaci a tabbatar da adalci da cika alkawuran diyya da aka yi masu
  • Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kibiya, Nasiru Adam Abdulaziz ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta Edo da su cika alkawari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Iyalan mafarautan jihar Kano da aka kashe a Edo sun sake rokon gwamnati da ta tabbatar da adalci, kwanaki 40 bayan kisan gilla da aka yi wa 'yanuwansu.

Mafarautan 16 daga ƙananan hukumomin Kibiya, Rano da Bunkure a jihar Kano ne aka kashe yayin da suke shirin zuwa gida yin Karamar Sallah.

Uromi
Iyalan mafarautan Kano da aka kashe a Uromi sun yi zanga-zanga Hoto: Sam digitalz/Fahd Muhammad
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa kisan ya tayar da hankula a fadin ƙasar nan, wanda ya jawo wasu sun fara bukatar gwamnati ta gaggauta hukunta wadanda suka aikata mugun aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi zanga-zanga kan kisan mafarautan Kano

Daily Post ta wallafa cewa a yayin sadakar 40 na mamatan, dangi da abokan arziki da mazauna yankin sun hallara a ginin sakatariyar ƙaramar hukumar Kibiya.

A nan ne aka gudanar da addu’ar domin kara nemawa mamatan rahamar Allah, daga bisani kuma aka gudanar da zanga-zanga.

Malam Bala Dutse, mahaifin Amadu daya daga cikin mafarautan da aka kashe, ya bayyana cewa ba su samu wani bayani mai gamsarwa daga gwamnati ba har yanzu.

Jihar Kano
Iyalan Mafarutan Kano da aka kashe a Edo sun ce har yanzu ba a bi masu hakkinsu ba Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Ya ce:

“Babu wani sahihin bayani da muka samu. Gwamnati ya kamata ta yi magana da mu, ta bayyana shirin diyya idan akwai.”

Iyalan mafarautan Kano sun koka

Hauwa’u Isa, matar daya daga cikin mafarautan da aka kashe, ta roki gwamnati da ta cika alkawuran da ta dauka na diyya da adalci.

Ta ce:

“Sun ce za su yi adalci kuma za su ba mu diyya. Ina fatan hakan zai tabbata, amma ina fargabar kar ya zama alkawari ne babu cikawa.”

A jawabinsa, Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kibiya, Nasiru Adam Abdulaziz ya jaddada cewa gwamnati tana tare da iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar Edo da su cika alkawarin da suka ɗauka na bincike da hukunta masu laifi.

Majalisa ta magantu kan kisan mafarautan Kano

A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya goyi bayan kudurin da Sanata Kawu Sumaila ya gabatar dangane da kisan mafarautan Kano a jihar Edo.

Wannan batu ya taso a zaman majalisar dattawa na ranar Talata, inda Sanata Barau ya jaddada bukatar hukunta mutanen da suka yi wa Hausawan kisan killa domin a tabbatar da adalci.

Kisan da aka aikata a garin Uromi na jihar Edo cikin watan Maris ya girgiza kasa baki daya, inda mafarautan daga Kibiya, Rano da Bunkure suka rasa rayukansu a hanyarsu ta dawo wa gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.