Yan Sanda Sun Kama Buhuna 30 Na Tabar Wiwi a Jihar Legas

Yan Sanda Sun Kama Buhuna 30 Na Tabar Wiwi a Jihar Legas

  • Rundunar 'yan sandar jihar Lagos ta sanar da kama wani mutum dauke da buhun tabar wiwi guda 30 a yankin Ojo
  • A cewar mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin sun kama mutumin ne ranar Laraba da asuba
  • Ya kuma tabbatar da cewa yanzu haka sun zurfafa bincike wurin kamo sauran bata garin da suke harka da mutumin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta sanar da nasarar kama buhu 30 na wasu abubuwa da ake kyautata zaton tabar wiwi ne.

A cewar rundunar, ta kama kayan ne a yankin Ojo da ke Legas da misalin karfe 4.30 na safe.

Kara karanta wannan

Ana murna Dangote ya fara fitar da mai, sojoji sun tafka ta'asa a matatar, an dauki mataki

Lagos Police
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargi da zarar an kammala bincike. Hoto LagosPoliceng
Asali: Twitter

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Benjamin Hundeyin, ya ce jami'ansu da ke Ijanikan ne suka yi nasarar kama mutumin a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama mutumin

Jaridar the Cable ta ruwaito cewa jami'an 'yan sandan sun bi sawun wata mota ce kirar marsandi da ta ke tafiya zuwa Ojo.

A yayin da suke bin ta sai suka ga alamar abubuwa da suke zargi a kan tabar wiwi ce da aka saukewa daga wani jirgin ruwa.

Mista Hundeyin ya tabbatar da cewa matukin motar da ake zargin ya shiga hannun 'yan sanda sauran kuma ana binciken yadda za a kamo su.

Ya kuma tabbatar da cewa matukin motar da suka kama mai shekaru 43 sun same shi da buhun tabar wiwi guda 30.

Mutumin bai amsa laifi ba

Amma mutumin ya ce shi ma wani mutun ne mai suna Ifeanyi ya ba shi kayan a kan ya kai masa zuwa yankin Ojo, cewar jaridar the Gurdian

Kara karanta wannan

Kasar Yarbawa: Kotu ta rufe masu fafutukar raba Najeriya bisa zargin cin amana

Mai magana da yawun 'yan sandar ya ce yanzu haka bincike ya kankama a kan kamo mutumin da ya bawa matukin motar kayan.

An kama sojojin bogi a Legas

A wani rahoton kuma, kun ji cewa, rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta yi nasarar kama wasu mutum biyu dauke da makamai da su ke cewa su sojojin Najeriya ne.

A cewar rundunar, ta samu bayanan sirri ne a kan yadda mutanen suka yi kokarin hallaka wani mutum da wuka a kan titin Aina, Isolo da ke jihar kafin daga bisani su cafke su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel