Gwamna Ya Tono Tsuliyar Dodo da Ya Haramta Wa'azi, Malamai Sun Yi Masa Rubdugu
- Gwamna Chukwuma Soludo na Anambra ya haramta wa’azi a kasuwanni, yana mai cewa hakan na haddasa hayaniya da gurbatar iska
- A cikin wani bidiyo da ya karade intanet, Soludo ya ce duk malamin addini da aka kama yana wa’azi a kasuwa zai biya tarar N500,000
- Shugabannin addini sun caccaki matakin da Soludo ya dauka, suna masu cewa hakan cin zarafin ‘yancin addini ne kuma hari ne kan Kiristoci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Shugabannin addini sun soki gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo, kan haramta wa’azi da amfani da lasifika a kasuwannnin jihar.
Mun ruwaito Soludo ya ce wa’azin da ake yi a kasuwanni yana haddasa hayaniya da jawo gurbacewar iska, wanda ke damun ‘yan kasuwa.

Asali: Facebook
Anambra: Gwamna ya hana wa'azi a kasuwanni
A wani faifan bidiyo da Anambra Diaries ta wallafa a shafin X, anji Soludo ya na barazanar cewa duk wanda aka kama yana wa’azi a kasuwa zai biya tarar N500,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi ga ‘yan kasuwa da ake zaton na kasuwar Ochanja ne da ke a garin Onitsha, Soludo ya ce kasuwa ba coci ko wurin bauta ba ce.
Gwamnan ya kara da cewa masu wa’azi ba za su iya yin amfani da kasuwa a matsayin coci ba, don haka za a hukunta duk malamin addini da aka kama.
"Hana wa'azi hari ne ga Kirista" - Bishop ga Soludo
Sai dai wannan mataki ya jawo suka daga shugabannin addini da wasu ‘yan Najeriya, wadanda suka ce hakan cin zarafin ‘yancin addini ne.
Babban sakataren Bishops na kasa da kasa (IESB), Archbishop Osazee Williams, ya ce hana wa'azi a bainar jama'a hari ne ga addinin Kirista.
Da yake magana da jaridar Punch a ranar Lahadi, Archbishop Williams ya ce hana wa’azi a kasuwa zai hana mutane da yawa jin kalmar Ubangiji.
Ya ce wa’azi a kasuwanni yana canza halayen mutane, don haka matakin da gwamnan ya dauka na iya yin illa ga al’umma.
An nemi CAN ta kalubalanci umarnin Soludo

Asali: Twitter
Shi ma shugaban cocin Methodist na Najeriya a Legas, Most Rev. Isaac Olawuyi, ya ce matakin gwamnan cin zarafin Kiristoci ne kai tsaye.
Ya ce ya kamata ya yi gwamnan ya tuntubi shugabannin addini kafin daukar wannan mataki, maimakon haramta wa’azi gaba daya.
Olawuyi ya bukaci kungiyar CAN da PFN a Anambra su tashi tsaye domin kalubalantar dokar da gwamnan ya kafa.
Ya ce matakin gwamnan na iya hana Kiristoci cika umarnin Ubangiji na yin wa’azi a ko’ina, matukar ba a hana mutane sakewa ba.
Shugabannin addinin sun bukaci gwamnati ta nemo hanyoyin da za su takaita hayaniya ba tare da hana wa’azi gaba daya ba.
Kalli bidiyon Gwamna Soludo a nan kasa:
Gwamna ya rufe masallatai da majami'u
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Legas, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ta ce ta rufe wurare 352 a faɗin jihar saboda hayaniya a shekarar da ta gabata.
Cikin wuraren da aka rufe akwai masallatai, coci-coci, da sauran wuraren ibada na Musulmai da Kiristoci da kuma wasu gine gine da ke gurbata iska.
Asali: Legit.ng