Yadda 'Yan Bindiga Suka ba Karnuka Tagwayen Jarirai Suka Cinye a Dajin Zamfara

Yadda 'Yan Bindiga Suka ba Karnuka Tagwayen Jarirai Suka Cinye a Dajin Zamfara

  • Dan majalisar wakilai daga Zamfara, Aminu Jaji ya ce an kai wani mummunan matsayin da ‘yan bindiga ke bai wa karnukansu jariran da aka haifa a daji
  • Ya bayyana cewa wata mata da aka sace ta haifi tagwaye a cikin daji, sai shugaban ‘yan bindigar ya jefar da jariran ga karnuka, inda suka cinye su
  • Jaji ya bukaci a kara amfani da fasaha wajen yakar ‘yan ta’adda, yana mai cewa sojojin Najeriya na da karfin tinkarar matsalar idan aka karfafa musu guiwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kaura-Namoda/Birnin Magaji daga jihar Zamfara, Aminu Sani Jaji ya fadi yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a yankinsa.

Jaji, wanda dan jam’iyyar APC ne, ya bayyana wani mummunan lamari da ke nuna yadda rikicin da ake fama da shi a Arewa maso Yammacin Najeriya ke kara tsananta.

Tinubu
Yan bindiga sun ba kare naman jariri a Zamfara. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Punch ta rahoto cewa Jaji ya ce wata mata mai juna biyu da aka sace a kauyen su ta haihu a daji, sai shugaban ‘yan bindigar ya bai wa karnukansa jariran da ta haifa suka cinye su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun ciyar da karnuka naman jarirai

Da yake jawabi ga manema labarai a Majalisar Tarayya, Jaji ya bayyana cewa akwai bukatar daukar mataki cikin gaggawa kan abin da ke faruwa a Zamfara da sauran yankuna.

Vanguard ta rahoto ya ce:

“Wata mata da aka sace ta haifi tagwaye a daji. Shugaban ‘yan bindigar ya dauki jariran, ya jefar da su ga karnukansa. Karnukan suka ci jariran daya bayan daya.”

Jaji ya ce wannan lamari ya wuce tunani, yana mai kiran gwamnati da ta dauki kwararan matakai, domin kare lafiyar jama’a da mutuncin al’umma da ake wulakantawa.

Jaji: 'Sojoji na da karfin yakar 'yan bindiga'

Sai dai Jaji ya nuna rashin goyon bayansa ga kudirin shigo da mayakan haya don yaki da ‘yan ta’adda, yana mai cewa rundunar sojin Najeriya na da isasshen karfi.

Ya ce idan aka samar da kayan aiki na zamani da kula da jin dadin jami’an tsaro, za su iya kawar da ‘yan ta’adda ba tare da dauko wasu daga waje ba.

An sace fiye da mutum 200 a mazabar Jaji

Jaji ya bayyana cewa a mazabarsa kadai, 'yan bindiga sun sace fiye da mutum 200, ciki har da mutum 60 da aka dauka a Banga, inda aka kashe wasu 10 saboda rashin kudin fansa.

Ya kara da cewa akwai wasu mutane 25 da aka sace daga kauyen Gabake, sai kuma sabon harin da aka kai a Kungurki, wanda ya sake jefa al’umma cikin tashin hankali da fargaba.

'Dan majalisar ya koka kan yadda ‘yan bindiga ke tafiyar da yankunan da suka mamaye kamar gwamnati, suna cin karensu ba babbaka cikin kauyuka.

Tinubu
Jaji ya bukaci Tinubu ya kara inganta tsaro a Arewa ta Yamma
Asali: Facebook

Ya ce akwai yiwuwar shugaban kasa Bola Tinubu ba ya samun cikakken rahoto game da halin da yankin ke ciki, yana mai bukatar sake fasalin tsarin tsaron kasa gaba daya.

Za a yaki 'yan bindigar da suka fake a daji

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai dauki dubban matasa aiki domin magance matsalar tsaro.

Gwamnatin tarayya za ta yi hadaka da jihohi wajen daukan matasa aikin domin fatattakar 'yan ta'adda a dazuka.

Ma'aikatar muhalli ta kasa ta ce gwamnatin Bola Tinubu ba za ta bar wani yanki na kasar a karkashin 'yan ta'adda ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng