BUA Ya Yi Maganar Saukar Farashin Abinci da Siminti bayan Ganin Tinubu a Aso Villa

BUA Ya Yi Maganar Saukar Farashin Abinci da Siminti bayan Ganin Tinubu a Aso Villa

  • Kamfanin BUA da Dangote sun amince da daidaita farashin siminti ga dukkan ‘yan kwangila da ke aiki ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Shugaban BUA, Abdul Samad Rabiu, ya ce wannan matakin yana daga cikin gudunmawar da suke bayarwa wajen tallafawa kokarin farfado da tattali
  • Abdul Samad Rabiu ya bayyana cewa farashin kayan abinci ya ragu sosai idan aka kwatanta da bara, sakamakon shigo da kayayyaki daga ketare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanonin BUA da Dangote sun dauki sabon mataki na rage radadin tsadar kayan gini a Najeriya ta hanyar daidaita farashin siminti ga ayyukan gwamnati.

Shugaban BUA, Abdul Samad Rabiu ne ya sanar da haka bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025.

Tinubu
Kamfain BUA ya yi maganar sauke farashi bayan haduwa da Tinubu. Hoto: @BUAGroup
Asali: Twitter

Kamfanin BUA ya tabbatar da ganawar a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdul Samad Rabiu ya bayyana cewa wannan mataki yana da nufin rage yawan kudin da ake kashewa wajen aiwatar da manyan ayyuka a fadin kasar nan.

BUA ya ce za a hana farashin siminti tashi

BUA ya ce sun cimma yarjejeniya da shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, wajen tabbatar da cewa ba za a kara farashin siminti ba a duk ayyukan gwamnatin tarayya.

Vanguard ta wallafa cewa shugaban BUA ya ce:

"Mun yanke shawarar daidaita farashin siminti ga duk wata kwangila da ke da hannu a ayyukan gwamnatin tarayya.
"Wannan shi ne gudumuwar da muke bayarwa ga kokarin Shugaba Tinubu,"

Ya kara da cewa an sake fasalin kungiyar masu hada siminti ta kasa (CEMAN), inda aka nada Injiniya Yusuf Binji na BUA a matsayin sabon shugaban kungiyar.

Bayani kan horar da magina a Najeriya

BUA ya ce za a samar da tallafin kudi daga ₦15bn zuwa ₦20bn duk shekara don ciyar da Cibiyar Fasahar Siminti ta Najeriya (CTIN), wadda ke horar da masu aikin gini a fadin kasar nan.

Za a ciro wannan tallafi ne daga cajin ₦20 zuwa ₦30 da za a kara kan kowane buhun siminti da ‘ya’yan kungiyar CEMAN ke sayarwa.

Batun saukar farashin abinci a Najeriya

Abdul Samad Rabiu ya bayyana yadda shirin gwamnatin tarayya na karbar kayan abinci daga waje ba tare da biyan haraji ba na wata shida ya taimaka wajen karya farashin abinci.

Tinubu
BUA: Abdulsamada Rabiu ya yi maganar rage farashin abinci da siminti bayan haduwa da Tinubu
Asali: Facebook

Ya ce BUA ya shigo da shinkafa, masara da alkama da yawa, wanda hakan ya rage farashin kaya kamar shinkafa da ta ragu daga ₦110,000 zuwa ₦60,000, da alkama daga ₦80,000 zuwa ₦55,000.

Attajirin ya gode wa Shugaba Tinubu bisa hangen nesa da yake yi, yana mai cewa BUA za ta ci gaba da bayar da gudumawa domin tallafawa tattalin arziki da walwalar al’umma.

Legit ta tattauna da manomi a Gombe

Wani manomi a jihar Gombe ya ce duk da ya yi noma sosai, ba ya bakin ciki da saukar farashin kayan abinci.

Muhammad Ahmad ya ce:

" Bai kamata a yi bakin ciki don an samu sauki ba. Kawai dai ya kamata a sauke farashin sauran abubuwa ne kamar taki da fetur ga masu noman rani.
"Matukar ba a samu saukinsu ba, to mutane za su daina noma sosai a Najeriya."

Masu casar shinkafa sun koka da saukar farashi

A wani rahoton, kun ji cewa wasu masu boye abinci a Najeriya sun koka kan yadda farashi ya karye a shekarar bana watau 2025.

Wani mai sayar da shinkafa ya ce abokinsa ya karbi bashin miliyoyin kudi ya saye abinci amma kasuwa ta juya masa baya.

Masu harkokin casar shinkafa sun bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta dawo da tsarin shigo da abinci da gwamnatin Buhari ta kawo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng