Farashin Siminti Ya Sauko Bayan FG Ta Sa Ba, An Gano Jihohin da Buhun Ya Fi Arha

Farashin Siminti Ya Sauko Bayan FG Ta Sa Ba, An Gano Jihohin da Buhun Ya Fi Arha

  • Binciken da aka yi kwanan nan a jihohin Najeriya ya nuna cewa farashin siminti ya ragu amma ya danganta da kamfani
  • Manyan kamfanonin siminti uku na sahun gaba suna siyar da kayansu a farashi daban-daban yayin da diloli ke sa farashin ƙarshe
  • Rahoton binciken ya nuna cewa farashin simintin ya ragu a Abuja, Nasarawa da Neja biyo bayan sa bakin da gwamnatin tarayya ta yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Farashin siminti ya ragu a wasu jihohin Arewacin Najeriya, inda ya dawo N8,000 zuwa N9,500 kan kowane buhu ɗaya.

Wannan sauƙi da aka samu na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta tsoma baki, amma duk da haka siminti ya fi tsada a Najeriya idan aka kwatanta da sauran ƙasashen Afirka.

Kara karanta wannan

N11,000/50kg: Hauhawar farashin siminti da matsalolin da yake haifarwa a Najeriya

Farashin siminti ya ragu a wasu jihohi.
Farashin Siminti Ya Sauko Bayan FG Ta Sa Ba, An Gano Jihohin da Buhun Ya Fi Arha Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Facebook

Jihohin da buhun siminti ya fi arha

Wani bincike da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa manyan kamfanoni irin su Dangote, Lafarge da BUA suna sayar da simintin a kusan farashi daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin siminti ya ragu a birnin tarayya Abuja, Neja da jihar Nasarawa idan aka kwatanta da farashin da ake sayar da shi sama da Naira 13,000 kan kowane buhu kafin gwamnati ta sa baki.

Bincike ya nuna cewa ana siyar da simintin Dangote kan N8,000 da N9,500, Simintin Lafarge N8,000 da N9,300, sai kuma simintin BUA ya kai N7,500 da N9,000.

‘Yan kasuwa sun bayyana ra’ayoyinsu kan yadda kasuwar siminti ke tafiya bayan umarnin gwamnati ga masana’antun na rage farashin da kusan kaso 50%.

Ƴan kasuwa sun ce farashin siminti zai kara raguwa

'Yan kasuwan sun ce farashin na iya kara raguwa amma a yi taka-tsan-tsan saboda masana'antu, masu sayar da kayayyaki, da dillalai ke da wuƙa da nama wajen saita farashi ga kwastomomi.

Kara karanta wannan

"Mijina ya daina kwana da ni a gado" Matar aure ta cire kunya ta fashe da kuka a kotu

A cewarsu, ana samun banbancin farashi ne tun daga wurin da aka siyo kaya, inda wasu ke alaƙa kai tsaye da masana'antun, wasu kuma ta hanyar dillalai.

Masu tsohon kaya ne kaɗai ke siyar da buhun siminti a farashin N9,500, N8,500 ko N8,000.

Karancin mai ya ɓulla a Abuja

A wani rahoton na daban Ƙarancin man fetur na kara kamari a Abuja yayin da aka fara dogayen layuka ranar Jumu'a, 8 ga watan Maris, 2024.

Masu ababen hawa da direbobin motocin haya sun haɗa dogon layi a wasu gidajen mai, wasu kuma sun kulle sun daina siyarwa jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel