Farashin Shinkafa, Masara da Gari Ya Faɗi Warwas, BUA Ya Gargadi Masu Boye Abinci

Farashin Shinkafa, Masara da Gari Ya Faɗi Warwas, BUA Ya Gargadi Masu Boye Abinci

  • Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya ce za su ci gaba da rage farashin shinkafa, sakamakon sauƙin haraji daga gwamnati
  • Ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa dakatar da harajin kwastam a 2024, yana mai cewa hakan ya rage tsadar shinkafa da masara sosai
  • Abdul Samad ya bayyana yadda masu adana shinkafa ke haddasa hauhawar farashi, amma ya yi alkawarin ci gaba da karya fashin abinci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya sha alwashin kara rage farashin shinkafa da sauran kayan abinci da ya ce tuni sun fara raguwa.

Ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa sassauta harajin kayayyakin abinci da ake shigowa da su daga waje, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen faduwar farashin abinci a kasar.

Shugaban kamfanin BUA, ya ce farashin shinkafa, masara da gari ya sauka sosai
Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu. Hoto: @BUAgroup
Asali: Facebook

"Farashin shinkafa ya fadi" - BUA

A watan Yulin 2024 ne gwamnatin Tinubu ta dakatar da karbar harajin kwastam kan kayan abinci da ake shigo da su, domin rage hauhawar farash, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, Abdul Samad ya bayyana cewa BUA Foods ta yi amfani da wannan damar wajen shigo da alkama, masara da shinkafa da dama.

“A lokacin, farashin kayan abinci ya yi tsada matuka. Misali, buhun shinkafa mai kilo 50 ya kai kusan N100,000. Gari ya kai N80,000, masara kuma N60,000, sannan kwalin taliya ya wuce N20,000. Don haka, muka yi amfani da damar, muka shigo da alkama, masara da shinkafa.
“Daga lokacin da kayayyakin suka fara shigowa, muka fara sarrafa su, muka karya farashin wasu daga cikin wadannan kaya.
"A yau, ina farin cikin sanar da ku cewa farashin shinkafa ya koma kusan N60,000 daga N110,000 da aka sayar da ita a bara. Gari yanzu yana kusan N55,000."

- Abdul Samad BUA.

'Masu boye abinci ke jawo tsadar shi' - BUA

Hamshakin attajirin ya kara da bayyana wasu daga cikin abubuwan da suka haddasa tashin farashin abinci da yadda tsarin shugaban kasa ya taimaka wajen dakile hauhawar.

Shugaban kamfanin BUA ya ce masu boye abinci ke jawo tsadar kayan abinci
Wasu ma'aikata na aiki a kamfanin sarrafa shinkafa. Hoto: Bahati
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta rahoto Abdul Samad BUA ya kara da cewa:

“Abin da ke faruwa, wanda da dama ba su sani ba, shi ne, kamfanoni da dama a Najeriya suna sayen shinkafa daga gona tun a lokacin girbi.
"Su kan saya da yawa su ajiye na tsawon watanni uku zuwa hudu. Da zarar damina ta kare, sai farashin shinkafar ya nunka. Wannan shi ne matsalar da ake fama da ita.
“Wannan matsalar ba da manomi ba ne, domin yana samun N400,000 zuwa N500,000 a kowanne tan. Amma masu siye da ajiye kaya ne ke janyo hauhawar farashin zuwa kusan N800,000. Daga nan ne ake samun buhu daya ya kai N110,000.

Farashin shinkafa ya karye a kasuwar Enugu

A wani labari, mun ruwaito cewa, farashin shinkafar gida mai kyau ya sauka a jihar Enugu, inda yanzu buhu mai nauyin 50g ake sayar da shi ƙasa da N78,000.

Masu sayar da shinkafa a Enugu sun shawarci jama'a da su yi amfani da wannan lokacin don sayen shinkafa da yawa kafin farashinta ya sake ƙaruwa.

Jama'a a jihar Enugu sun nuna farin cikinsu game da saukar farashin, saboda hakan zai ba su damar yin bukukuwa cikin wadatar abinci, sabanin a lokacin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.