Ministoci za Su Tafi London Nunawa Duniya Ayyukan da Tinubu Ya Yi a Najeriya

Ministoci za Su Tafi London Nunawa Duniya Ayyukan da Tinubu Ya Yi a Najeriya

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike da na Ayyuka, Dave Umahi za su jagoranci taron manema labarai a London don bayyana nasarorin Bola Tinubu
  • An shirya kaddamar da kundin ayyuka da shafin yanar gizo da ke dauke da jerin muhimman ayyuka da gwamnatin Tinubu ta kammala a shekaru biyu
  • Shugaban kungiyar Tinubu Consolidation Mandate, Bode Adeyemi, ya ce taron zai bai wa duniya damar fahimtar sahihan nasarorin da aka cimma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT Abuja - Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta gabatar da taron manema labarai a ƙasar Ingila domin bayyana nasarorin da ta cimma cikin shekaru biyu na mulkinta.

Taron da aka shirya gudanarwa a London zai haɗa da ministoci da shugabannin hukumomi daga sassa daban-daban na gwamnati.

Tinubu
Ministoci za su nuna nasarar da Tinubu ya samu a birnin London. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa shugaban kwamitin duba muhimman ayyuka na Tinubu kuma shugaban kungiyar Tinubu Consolidation Mandate, Bode Adeyemi ne ya fadi hakan a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministocin da za su gabatar da jawabi a London

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike da na Ayyuka, Dave Umahi, na daga cikin manyan jami'an da za su gabatar da nasarorin ma'aikatunsu.

Sauran da ake sa ran za su gabatar da jawabi sun haɗa da Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo; Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur, Gbenga Komolafe.

Jaridar Tribune ta rahoto cewa Shugaban Hukumar Haraji ta Ƙasa, Zacheous Adedeji ma zai gabatar da jawabi.

Bode Adeyemi ya ce an tattara bayanai cikin tsanaki domin tabbatar da cewa ana gabatar da sahihan nasarori da za su gamsar da 'yan Najeriya da ma kasashen waje.

Abuja
Wike zai gabatar da jawabi kan gwamnatin Tinubu a London. Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Za a kaddamar da kundin ayyukan Tinubu

Adeyemi ya bayyana cewa kundin ayyuka na musamman da gwamnatin Tinubu ta aiwatar cikin watanni 24 zai kasance wani muhimmin bangare na taron.

Haka kuma za a kaddamar da shafin yanar gizo na musamman da ke dauke da bayanai kan manyan ayyuka da aka kammala da kuma wadanda ake cigaba da yi.

Ya ce duk da matsalolin tattalin arzikin duniya da kalubalen da ke fuskantar Najeriya, gwamnatin Tinubu ta ci gaba da yin fice da nasarori a fannoni da dama.

Muhimmancin taron ga martabar Najeriya

Shugaban jam'iyyar APC reshen Birtaniya, Tunde Doherty, ya ce matakin da aka dauka yana da muhimmanci sosai.

Ya ce hakan zai taimaka wajen bayyana sahihan bayanai ga duniya da kuma dakile yaɗuwar ƙarya da yaɗuwar jita-jita daga bangaren adawa.

A cewarsa, wannan taro zai taimaka wajen kare mutuncin Najeriya da tabbatar da cewa ana yada sahihan labarai kan abin da ke gudana a mulkin Tinubu.

Oshiomhole ya ce Tinubu ya yi ayyuka sosai

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole ya ce Bola Tinubu ya yi ayyuka sosai.

Adams Oshiomhole ya ce shugaban kasar ya yi ayyuka da suka shafi tattalin arziki da inganta tsaron Najeriya.

A karkashin haka ya ce yana da tabbas a kan cewa Bola Tinubu zai samu nasara a zaben shekarar 2027 da ake fuskanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng