'Mun Ci Bashin Miliyoyi,' Masu Boye Abinci Suna Kuka da Karyewar Farashin Hatsi
- Masu boye hatsi a jihar Neja suna tafka babbar asara bayan da farashin hatsi ya rika faɗuwa maimakon tashi kamar yadda suka yi zato
- Wasu ‘yan kasuwa sun karɓi bashin miliyoyin Naira daga bankuna ko sun sayar da kadarorinsu don sayan hatsi da fatan samun riba daga tashin
- Rahotanni sun nuna masu amfani da kayayyaki na murna da saukar farashi, suna cewa hakan wata rahama ce daga Allah domin rage musu wahala
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - An samu koma baya ga masu boye hatsi a jihar Neja bayan da farashin kayan abinci ya ci gaba da faɗuwa tun watan Oktoba 2024 zuwa yanzu.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan kasuwa sun sayi hatsi irinsu wake, masara, gyada, gero da dawa da zimmar samun riba, amma kasuwar ta juya musu baya.

Asali: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa wasu ‘yan kasuwa sun karbi bashi ko sun sayar da kadarorinsu domin boye kayan abinci, amma yanzu suna cikin damuwa sakamakon faɗuwar farashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu amfani da hatsi sun yi murna
A kasuwannin karkara kamar Zungeru, Beji, Kakakpangi, Lapai, Manigi, Lemu da Wuya, farashin wake, dawa da masara suna ci gaba da raguwa.
Wani kwastoma a kasuwar Kure, Victor Ejike, ya bayyana cewa rahamar Allah ce ta saukar da farashin, yana mai cewa gwamnati bata da hannu cikin saukar farashin kayan abinci.
Ejike ya ce:
“A bara, muna siyan mudu ɗaya na wake a N3,500, amma yanzu na sayi mudu ɗaya a N1,600. Wannan sauƙi ne daga Allah.”
Masu boye hatsi na tafka asara
Masu boye hatsi irin su wake, masara, dawa da gero sun bayyana cewa suna fuskantar asara sosai bayan da kasuwa ta ki amsa hasashensu.
Wani ɗan kasuwa ya bayyana cewa abokinsa ya karɓi bashin Naira miliyan 20 daga banki domin sayan hatsi lokacin girbi, amma yanzu farashin ya faɗi ƙasa matuƙa.
A kananan hukumomin Manigi, Mashegu ana sayar da buhun jan wake a N100,000, farin wake N95,000, masara N45,000, da dawa a N50,000.

Asali: UGC
Kasuwa ta yi kyau da wadanda suka boye gyada
Bincike ya nuna cewa masu boye egusi da gyada ne kaɗai ke samun riba daga cinikin su a halin yanzu a kasuwanni daban-daban.
Ana sayar da buhun egusi yanzu a N62,000 sabanin N40,000 da aka sayo lokacin girbi, yayin da gyada ke kai N30,000 zuwa N40,000.
Sai dai, masu boye waken suya, masara, dawa da gero sun bayyana cewa asarar da suka yi na iya durƙusar da harkokinsu gaba ɗaya, musamman waɗanda suka dogara da bashin banki.
Legit ta tattauna da manomi a Gombe
Wani manomi a jihar Gombe, Shuaibu Muhammad zantawa Legit cewa ba ya bakin ciki da saukar farashin kayan abinci.
Manomin ya ce:
"Babban abin da ya kamata a yanzu shi ne sauke farashin taki. Idan farashin taki bai sauka ba, ba kowa ne zai yi noma ba a bana.
"Idan ba a yi noma sosai ba kuma za a iya komawa gidan jiya."
Farashin abinci ya karye a Arewa maso Gabas
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan kasuwa sun bayyana dalilin samun sauki da karyewar kayan abinci a Arewa maso Gabas.
Hakan na zuwa ne bayan an farashin gero, masara, shinkafa da wake na cigaba da karyewa a kasuwa.
Wasu 'yan kasuwa sun bayyana cewa rashin jari a hannun mutane, raba kayan abinci da aka yi da noma da mutane suka yi na cikin dalilan karyewar farashin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng