Dan Siyasar da Ke Zaune a Amurka Ya Samu Takarar Majalisar Wakilai a ADC
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta ba wani dan siyasa da ke zaune a Amurka tikiti takarar dan majalisar tarayya a zaben 2027
- An tabbatar da cewa Emeka Bahadur, ya zama ɗan takarar ADC na mazabar Ikwuano/Umuahia ta tarayya gabanin zaɓe mai zuwa
- Jam’iyyar ADC ta amince da Bahadur ta hanyar masalaha bayan mambobi sun amince da tsarin kaɗa kuri’ar murya wajen zaɓen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia - Hon. Emeka Bahadur mai zama a ƙasar Amurka ya zama ɗan takarar jam’iyyar ADC na mazabar Ikwuano/Umuahia ta tarayya a Abia.
Bahadur ya samu tikitin takarar ne bayan shugabannin jam’iyya da mambobi suka amince da tsarin masalaha wajen zaɓen ɗan takarar mazabar.

Source: Facebook
Chinweikpe Joseph ne ya gabatar da ƙudirin amfani da kuri’ar murya daya yayin da Sunny Nwagboo ya mara masa baya a taron, cewar Punch.
Godiya da Emeka Bahadur ya yi ga ADC
Da yake jawabi bayan bayyana sunansa a Umuahia, Bahadur ya gode wa shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki kan goyon baya.
Ya kuma yabawa mata da matasa da suka halarci taron tare da bayyana hakan a matsayin babban tarihi ga makomar mazabar tasu.
Bahadur ya ce idan aka ba shi damar wakiltar al’umma a majalisar tarayya zai yi aiki domin ci gaban mazabar da jihar.
Ya ce:
“Idan aka ba ni damar wakiltar Ikwuano/Umuahia a Majalisar Tarayya, zan sanya mazabar da daukacin jihar su yi alfahari ta hanyar wakilci mai amfani ga jama’a.
“Abin da na gani yau ya sa na yi alfahari da maza da mata da matasan da suka fito da yawa domin nuna goyon baya ga wannan tafiya.”

Source: Original
Yan ADC sun yi murna kan nasarar Bahadur
Ya bayyana cewa abin da ya gani daga taron ya nuna yadda jama’a ke da ƙwarin guiwar ganin sauyi a yankin nasu, cewar Daily Post.
Magoya bayan jam’iyyar ADC sun yi murna tare da rera wakoki bayan sanar da Bahadur a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a mazabar.
Wasu daga cikin mambobin jam’iyyar sun bayyana wannan mataki a matsayin sabon babi na siyasa ga al’ummar Ikwuano/Umuahia a Abia.
Bahadur ya jaddada cewa zai mayar da hankali kan wakilci nagari da manufofin da za su amfani talakawan yankin idan aka zaɓe shi..
Kwara: An dakatar da zaben fitar da gwani
Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC a Kwara ta dakatar da zaɓen fitar da gwani na gwamna da aka shirya yi a yau Alhamis 21 ga watan Mayun shekarar 2026.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan ya biyo bayan rikici da ruɗani sun dabaibaye jam’iyyar yayin da aka fara kaɗa ƙuri’a.
Shugabannin APC sun ce umarnin dage zaɓen ya fito daga hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa, yayin da ruɗani ya ci gaba tsakanin magoya baya.
Asali: Legit.ng

