'Yan Sanda Sun Tare Hanya, An Cafke Matar da ke Kai wa Ƴan Bindiga Makamai a Arewa
- Rundunar ’yan sandan Nasarawa ta kama Fatima Salisu mai shekara 21 bisa zargin safarar makamai zuwa hannun ’yan ta’adda
- An tare Fatima a Lafia tana wucewa Keana da Doma, inda aka gano harsasai 481 a motarta, bisa bayanan sirri da aka tattara
- ’Yan sanda sun ce bincike na ci gaba, kuma wannan kama babbar nasara ce a yaki da safarar makamai da ta’addanci a Arewa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Nasarawa - Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wata Fatima Salisu, 'yar shekara 21, wadda ake zargi da safarar makamai ga 'yan ta'adda a Katsina
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa an kama Fatima Salisu a unguwar Azuba da ke Lafia bisa bayanan sirri da suka samu.

Asali: Twitter
An cafke matar da ke safarar makamai
Fatima Salisu, ’yar asalin garin Funtua ce a jihar Katsina, kuma an tare ta ne a yayin da take ketare yankunan Keana da Doma, domin kai harsasai ga masu laifi, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan samun bayanai, kwamishinan ’yan sanda, Shetima J. Mohammed, ya ba sashin yaki da garkuwa da mutane umarnin gaggauta kama Fatima Salisu.
A lokacin kamen, ’yan sanda sun gano harsasai 400 masu tsayin 7.62x39mm da 81 masu tsayin 7.62mm kirar NATO a cikin motar Fatima Salisu da ta ke kokarin boyewa.
Kakakin 'yan sanda ya ce ana ci gaba da tsare da ita a yanzu, inda take fuskantar tuhuma sosai don gano ko tana da alaka da sauran masu safarar makamai a Arewacin Najeriya.
An sace akalla mutane 53 a Funtua, Dandume
DSP Nansel ya ce kama Fatima Salisu wani babban ci gaba ne a yaki da yaduwar makamai ba bisa ka’ida ba da ke haddasa ta’addanci da karfafa ayyukan ’yan bindiga.
A farkon watan Afrilu, an rahoto cewa an sace mutane akalla mutane 53, kuma an kashe akalla mutane 6 a hare-haren da aka kai a Funtua da Dandume da ke jihar Katsina.
Harsasan da aka kama na daga cikin nau’in da ake amfani da su a bindigar AK-47 da wasu bindigogin soja, abin da ke nuni da hadarin safarar makamai a jihohin.
Jami’an sashen yaki da garkuwa da mutanen na binciken inda harsasan suka fito, yayin da suke zargin akwai alakar matar da manyan kungiyoyin safarar makamai a Arewa.

Asali: Twitter
'Yan sanda sun nemi taimakon jama'a
Rundunar ’yan sandan Nasarawa ta bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai don ci gaba da murkushe miyagun mutane, inji rahoton Punch.
An bayyana wannan aiki a matsayin babbar nasara a yunkurin jihar Nasarawa na katse hanyar shigar makamai zuwa hannun masu tayar da kayar baya.
’Yan sanda sun kara jaddada kudurinsu na hana ayyukan masu laifi a Nasarawa, suna mai cewa za su bi duk wata sahihiyar hanya don cimma hakan.
'Yan sanda sun cafke dattijuwa da harsasai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta cafke wata mata mai suna Hamsatu Modu, ’yar shekara 54, a kauyen Morami da ke Konduga, jihar Borno.
An kama Hamsatu ne bisa zargin safarar harsasai 350 daga Buni Yadi da ke jihar Borno zuwa Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Kakakin ’yan sandan Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da cewa an kama matar ne a ranar Lahadi yayin da take kan hanyar safarar harsasan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng