EFCC ta cafke gungun matasa 'yan damfara a jihar Ogun
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki ta'anati, EFCC tayi nasarar cafke wasu matasa sama da 15 da ake tuhuma da laifuka da suka shafi damfara, sata, zamba cikin aminci da sauran su.
An kama matasan ne a ranar Asabar 3 ga watan Febrairun 2018 a unguwanin Shotubo da Awoluwo da ke yankin Sagamu da jihar Ogun bayan jami'an hukumar ta EFCC sun sami wasu bayyanan sirri da ke nuna cewa matasan na rayuwa ta alfarma duk da cewa babu wata sana'a da sukeyi.
An same su da kayayaki kamar na'urar komfuta, wayoyin salula dauke da takardun boge, motocin alfarma guda 6, laya da guru, layin kirar waya da sauran su.
KU KARANTA: Saraki ya karaya a kan shari'ar sa bayan gabatar da shaida daya katchal
Haka zalika, hukumar kuma tayi nasarar kai samame gidan wani boka da ake zargin yana taimaka wa matasan wajen tsafi da damfarar al'umma, an sami akwatin saka gawa, kwarya da kuma layyu a gidan nasa.
Hukumar za ta kai su kotu da zarar an kamalla bincike.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng