EFCC Ta Kama 'Yan China 13 Saboda Hakar Ma'adinai Ba Bisa Ka'ida Ba a Jihar Kwara

EFCC Ta Kama 'Yan China 13 Saboda Hakar Ma'adinai Ba Bisa Ka'ida Ba a Jihar Kwara

  • Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC), ta kama wasu 'yan ƙasar China 13 a jihar Kwara
  • Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutanen ne bisa laifin haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba
  • EFCC ta ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama ba sa da takardar izinin yin aiki a Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ilorin, Kwara - Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC) ta ce ta kama wasu 'yan ƙasar China 13 saboda haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a jihar Kwara.

Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwijaren ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a shafin EFCC na Tuwita.

Hukumar ta ce an kama mutanen da suka ƙunshi maza 12 da mace ɗaya a yankin GRA da ke Illorin babban birnin jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Miji Da Mata Sun Yi Basajar Shiga Musulunci Yayin Da Suka Tafkawa Liman Sata a Yobe

EFCC ta kama 'yan China 13 saboda hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba
EFCC ta kama wasu 'yan kasar China 13 bisa laifin hakar ma'adinai ba tare da izini ba. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kama su saboda haƙar ma'adinai ba tare da izini ba

Hukumar ta EFCC ta ce bayanan da ta samu kan ayyukan da mutanen ke aikatawa ta ƙarƙashin ƙasa da kuma rashin biyan kuɗaɗen haraji ga Gwamnatin Tarayya.

Kamar yadda EFCC ta bayyana, laifin da suka aikata ya saɓa da sashe na 1(8) (b) na kundin laifuka na 1983.

A yayin da aka tuhumesu, sun amsa cewa suna aiki ne ga wani kamfani mai suna W. Mining Global Services Limited, da ke a Olayinka a ƙaramar hukumar Ifelodun da ke jihar ta Kwara.

Wasu daga cikin ma'aikatan ba su da izinin aiki a Najeriya

EFCC ta ƙara da cewa kamfanin na sarrafa sinadarin giranayit ne domin samar da tayils da suke siyarwa a kasuwannin cikin gida.

A yayin da ake gudanar da bincike, an gano cewa wasu daga cikin ma'aikatan 'yar ƙasar China da aka kama ba sa da takardar izinin yin aiki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Yi Tonon Silili, Ya Bayyana Ainihin Masu Kashe Al'umma a Jiharsa

Hukumar ta ce za a gurfanar da su a gaban ƙuliya da zarar an kammala bincike.

Tsohon sanata ya garzaya kotu don hana EFCC bincikarsa

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cewa tsohon sanatan Bauchi ta Arewa, Muhammed Adamu Bulkachuwa, ya je kotu don neman hana EFCC da sauran hukumomi kama shi.

An bayyana cewa sanatan ya nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta hana hukumomi bincikarsa kan kalaman da ya yi a lokacin da yake majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng