Hukumar NEMA Ta Kawo Jerin Jihohi 14 da Za a Fuskanci Ambaliyar Ruwa Kwanan Nan

Hukumar NEMA Ta Kawo Jerin Jihohi 14 da Za a Fuskanci Ambaliyar Ruwa Kwanan Nan

  • Wani jami’in NEMA ya fitar da sanarwa cewa a shiryawa ambaliya da za ta barke ba da dadewa ba
  • Ibrahim Farinloye ya shaida cewa binciken masana ya nuna za ayi fama da annobar a wasu garuruwa
  • Hukumar bada agajin gaggawan ta nuna mafi yawan garuruwan nan su na yankin Arewacin Najeriya

Lagos - Hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa ta jero wasu garuruwa a jihohin Najeriya da ake da yiwuwar fuskantar ambaliya.

A rahoton Daily Trust na ranar Laraba, an samu labari cewa amabliyar ruwan da za ayi fama da ita a shekarar nan. Za ta shafi jihohi 14.

Wannan annoba za ta shafi kusan 40% na jihohin kasar nan kamar yadda sanarwar da hukumar ta NEMA ta fitar a makon nan ya nuna.

Ambaliyar Ruwa Kwanan Nan
Ambaliya a Najeriya Hoto: Getty / PIUS UTOMI EKPEI
Asali: Getty Images

Ibrahim Farinloye ya yi jawabi

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Hukumar NUC Ya Fadi Dalilin Rubuta Murabus, Ya Ajiye Mukaminsa

Jawabin jan-kunnen ya fito ne daga ofishin Mista Ibrahim Farinloye wanda yake kula da harkokin NEMA a ofishinta na shiyyar Legas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ibrahim Farinloye ya bukaci wadanda abin ya shafa a jihohin da aka ambata su dauki matakai na rigakafi domin kare rayuka da dukiya.

Idan an samu irin wannan masifa, ya kan zo da asarar dukiya na gidaje, amfanin gona har zuwa rayukan dabbobi da kuma Bil Adama.

Jaridar ta ce an kawo garuruwan da ake tunanin za a iya ambaliyar, kuma bincike ya nuna annobar za ta fi aukuwa ne a yankin Arewa.

Delta da Akwa Ibom ne kurum jihohin yankin Kudancin Najeriya da za a fuskanci amabaliyar ruwa nan da wasu ‘yan kwanaki kadan.

Jihohin da aka jero

1. Filato: Langtang, Shendam

2. Kano: Sumaila, Tudun wada

3. Sokoto: Shagari, Goronyo, Silame

Kara karanta wannan

Tsaro: Bukarti Ya Barranta Da Yerima, Ya Bayyana Matakin Da Ya Kamata A Dauka Akan 'Yan Bindiga

4. Delta: Okwe

5. Kaduna: Kachia

6. Akwa Ibom: Upenekang

7. Adamawa: Mubi, Demsa, Song, Mayo-belwa, Jimeta, Yola

8. Katsina: Katsina, Jibia, Kaita, Bindawa

9. Kebbi: Wara, Yelwa, Gwandu

10. Zamfara: Shinkafi, Gummi

11. Borno: Briyel

12. Jigawa: Gwaram

13. Kwara: Jebba

14. Neja: Mashegu, Kontagora

Farinloye ya yi godiya da jami’ansu na FEWS da ke ma’aikatar muhalli da ke bada irin wannan gargadi da su ka ankarar da al’umma da wuri.

Me yake jawo ambaliya?

Asheer Nababa Abdulmumin wanda masani ne a kan harkar tsara birane, ya yi wa Legit.ng Hausa bayanin abubuwan da ke kawo ambaliyar ruwa.

A cewarsa, rashin hanyoyin ruwa na cikin abubuwan da kan jawo ambaliya. Sannan ya alakanta annobar da sauyin yanayi da ake fuskanta a yau.

Wani dalili kuma shi ne ayyukan mutane kamar jefar da shara da yin gine-gine a kan a hanyoyin ruwa ko kuma tsukewar inda ruwa ya saba bi.

Badakalar Nigeria Air

Duk da biliyoyin kudin da aka kashe tsakanin 2016 da 2023, maganar ba ta kai ko ina ba, a wani rahoto da mu ka fitar, an ji gaskiyar abin da ya faru.

Hadi Sirika wanda ake yi wa kallon na hannun daman Buhari ne Ministan jirage a lokacin ne ake zargi ya yaudari shugaban kasa da gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel