Bayan Raba Awaki 40,000, Gwamna Ya Sake Rabawa Mata Buhun Shinkafa da N10,000

Bayan Raba Awaki 40,000, Gwamna Ya Sake Rabawa Mata Buhun Shinkafa da N10,000

  • Gwamnatin Katsina ta fara rabon tallafin kudi da kayan abinci ga zawarawa 7,220 da mata marasa galihu domin rage radadin rayuwa
  • Gwamna Dikko Radda ya kaddamar da shirin, inda mata 840 daga kananan hukumomi hudu suka fara amfana da shinkafa da ₦10,000
  • Gwamnatin ta ce an mayar da hankali kan zawarawa da mata marasa galihu domin ba su damar dogaro da kai da inganta rayuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta fara rabon tallafin kudi da kayan abinci ga zawarawa 7,220 da mata marasa galihu a fadin jihar.

Gwamna Dikko Umar Radda ne ya kaddamar da shirin a fadar gwamnati, a ranar Talata, inda aka bude labulen shirin da tallafawa mata 840.

Gwamnatin Katsina ta sanya farin ciki a zukatan zawarawa da marasa galihu
Gwamnatin Katsina ta kaddamar da shirin tallafawa mata da zawarara a fadin jihar. Hoto: @abdurlsheed
Asali: Twitter

Katsina: Radda ya rabawa zawara shinkafa da kudi

Matan sun fito daga kananan hukumomin Katsina, Kaita, Rimi, da Batagarawa, inda kowacce ta samu buhun shinkafa da ₦10,000, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yaki da 'yan bindiga: Jami'an sojoji sun kashe 'Gwamna' a jihar Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dikko Radda ya bayyana cewa wannan shiri yana cikin kudirin gwamnatinsa na tallafawa mabukata da rage radadin rayuwa a tsakanin al’umma.

“Wannan rana wata babbar alama ce ta burin gwamnatina na inganta jin dadin al’umma, musamman zawarawa da mata marasa galihu,”

- inji gwamnan Katsina.

Ya kara da cewa tallafawa wadannan mata ba kawai hakkin jama’a ba ne, har ma da sauke nauyin da ya rataya a wuyan gwamnatin jihar.

Radda ya fadi kalubalen da matan ke fuskanta

Gwamnan ya bayyana cewa matan da suka rasa mazajensu na fuskantar kalubale da suka hada da matsin tattalin arziki da wariya a cikin al'umma.

Ya ce an kirkiri shirin ne domin mayar da martabar wadannan mata tare da basu dama su taka rawa wajen cigaban jihar.

Dikko Radda ya ce:

“Ba nufin mu bayar da tallafin kudi kawai ba ne, muna kokarin samar da hanyoyin dogaro da kai ga mata, hanyoyi masu dorewa."

Kara karanta wannan

Rabuwar kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba su sa hannu a dakatar da Natasha ba

Ya jinjinawa hadin gwiwar ma’aikatun harkokin addini, ayyuka na musamman, harkokin mata da ci gaban al’umma wajen nasarar wannan shirin.

Mata a kananan hukumomi 34 za su samu tallafin

Gwamnan Katsina yayin da yake rabawa mata buhunan shinkafa da N10,000
Gwamnan Katsina, Dikko Radda yayin da yake ba wata mata tallafin N10,000 da buhun shinkafa. Hoto: @abdurlsheed
Asali: Twitter

Channels TV ta rahoto gwamnan ya bukaci masu cin gajiyar tallafin da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata don amfanin kansu da iyalansu.

“Muna fatan kudin da kayan abincin da kuka samu yau su zama tushen ci gabanku, ba kawai warware matsala na dan karamin lokaci ba,” in ji Radda.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa tana kokarin gina Katsina, ta yadda kowa zai samu dama ba tare da nuna wani bambanci ba.

A jawabinsa, Kwamishinan harkokin addini, Ishaq Shehu Dabai, ya ce an shirya tsarin ne don ya amfanin mata a duk kananan hukumomi 34 na jihar.

Ya ce an fi mayar da hankali kan zawarawa da marasa galihu domin rage musu radadin rayuwa da samar musu da hanyoyin dogaro da kai.

Kara karanta wannan

An fara cike fom domin samun tallafin noman Naira miliyan 1 na Sanata Barau

Radda ya rabawa matan Katsina awaki 40,000

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Dikko Raɗɗa ya kaddamar da shirin rabon awaki 40,000 ga mata da manoma domin inganta harkokin kiwo a jihar Katsina.

Gwamnan Katsinan ya bayyana cewa shirin, wanda zai ci Naira biliyan 5.7, zai ba mata da manoma damar samun horo kan kiwon zamani tare da tallafi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng