Bayan Sace Shugaban APC, 'Yan Bindiga Sun Rike Mutanen da Suka Je Karbo Shi

Bayan Sace Shugaban APC, 'Yan Bindiga Sun Rike Mutanen da Suka Je Karbo Shi

  • 'Yan bindiga sun tsare mutanen da suka kai kudin fansar shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Ose da ke jihar Ondo, Nelson Adepoyigi
  • An sace Adepoyigi da ke shugabantar jam’iyyar a gundumar Ifon ne a kofar gidansa da ke kan hanyar Ifon zuwa Owo, aka kai shi cikin daji
  • Bayan an rage kudin fansa daga Naira miliyan 100 zuwa miliyan 5, masu garkuwan sun tsare wadanda suka kai kudin domin kubutar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo- Ana ci gaba da fuskantar tashin hankali bayan wasu ‘yan bindiga sun sace shugaban jam’iyyar APC a gunduma ta 5 a Ifon cikin karamar hukumar Ose a jihar Ondo.

Bayan sun bukaci kudin fansa kuma aka tura wasu domin mika musu kudin, sai suka juya suka tsare su a cikin daji tare da kara bukatar karin kudi.

Jihar Ondo
'Yan bindiga sun kama wasu ceto shugaban APC a Ondo. Hoto: Legit
Asali: Original

Daily Trust ta wallafa cewa lamarin ya haifar da fargaba tsakanin ‘yan uwa, abokan aiki da mazauna yankin, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da kokarin ceto su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sace shugaban APC a kofar gidansa

Rahotanni sun nuna cewa an sace Adepoyigi ne da misalin karfe 10:00 na dare a ranar Litinin, a kofar gidansa da ke Ifon.

An bayyana cewa masu garkuwan sun janyo shi daga cikin motarsa tare da dukan sa da katako kafin su yi gaba da shi cikin daji.

Bayan faruwar lamarin, rundunonin ‘yan sanda da sojoji tare da masu sa kai da 'yan sintiri sun shiga daji domin farautar wadanda suka sace shi.

An rike wadanda suka je ceto shugaba a APC

A ranar Laraba da daddare ne aka tura Bayode Loco da Isimeri domin mika kudin fansar Adepoyigi bayan masu garkuwan sun amince da karbar Naira miliyan 5.

Sai dai wani daga cikin ‘yan uwansa ya shaida wa manema labarai cewa:

“Masu garkuwa sun tsare su duka biyun da suka kai kudin fansa, suna kuma bukatar karin N30m kafin su sako su baki daya.”

Halin da ake ciki a dalilin sace shugaban APC

Shugaban karamar hukumar Ose, Hon. Kolapo Oja, ya tabbatar da halin da ake ciki, yana mai bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan bindigar suka ci amanar yarjejeniyar da aka kulla da su.

Ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da ba hukumomin tsaro damar ci gaba da kokarin da suke yi na kubutar da wadanda ke hannun masu garkuwa da mutanen.

Yan sanda
Ana kokarin kubutar da shugaban APC da aka sace a Ondo. Hoto: Nigeria police Force
Asali: Facebook

Rahoton Tribune ya nuna cewa kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Ondo, SP Olusola Olayinka, ya ci tura.

Amma an tabbatar da cewa jami’an tsaro da masu sintiri na ci gaba da aiki dare da rana domin ganin an kawo karshen lamarin.

An kai hari kan makiyaya a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mutane dauke da bindiga sun kai hari kan wasu Fulani makiyaya a jihar Filato.

Maharan sun kashe wani makiyayi daya tare da jikkata da dama a cikinsu bayan kashe shanu sama da 100.

Yayin da take bayani, kwamishinar yada labarai ta jihar Filato ta ce za su yi bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng