Asirin Gungun Masu Hada Makamai Ya Tonu, 'Yan Sanda Sun Kama Mutum 4

Asirin Gungun Masu Hada Makamai Ya Tonu, 'Yan Sanda Sun Kama Mutum 4

  • Rundunar ‘yan sandan Jihar Enugu ta cafke wasu mutane da ake zargi da hannu a laifuffuka masu nasaba da safarar makamai da miyagun ƙwayoyi
  • An kama su ne a wasu ayyuka daban-daban, inda aka kwato bindigu guda biyu da kuma ganyen wiwi da ake zargin su da safararsu
  • Kwamishinan ‘yan sanda Mamman Bitrus Giwa ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaki da masu aikata laifuffuka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - Jami’an rundunar yan sandan Enugu sun sun cafke wani mai suna Ikechukwu Ugwele wanda aka fi sani da “Angle 90” mai shekara 35.

An cafke shi ne a ranar 9 ga Mayu, 2025, tare da kwato ganyen wiwi daga hannunsa, sannan daga baya ya jagoranci ‘yan sanda zuwa inda aka kwato wata bindigar kirar Beretta pistol.

Yan sanda
An kama wanda ake zargi yana hada bindiga a Enugu. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar the Nation ta wallafa cewa kakakin 'yan sandan jihar, Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar rundunar da Daniel Ndukwe ya fitar, wanda ake zargin ya amsa laifinsa tare da bayyana sauran laifuffukan da ya taba aikatawa a baya.

'Yan sanda sun kama masu hada bindiga a Enugu

A wani samame na dabam, jami’an Anti-Cultism Tactical Squad sun kama wani mai suna Emmanuel Eze wanda aka fi sani da “Camara” mai shekara 25 a ranar 8 ga Mayu.

Bayan kama shi, wasu mutum biyu, Uchenna Nwudi da Eze Chiadikobi sun amsa cewa suna cikin kungiyar asiri da yake jagoranta.

Nwudi ya amsa cewa shi ke kera bindigogi na gida, yayin da Chiadikobi ke da hannu a satar kayayyakin lantarki kamar su injin randar wuta ta transfoma.

Hakan na zuwa ne yayin da Najeriya ke cigaba da fuskantar kalubalen tsaro da suka hada da garkuwa da mutane da kai hare hare.

Kwamishinan ‘yan sanda ya yi magana

Kwamishina 'yan sandan jihar, Mamman Bitrus Giwa ya bayyana cewa tun bayan shigansa ofis a watan Maris, an kama mutum 291 da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban a Enugu.

Daga cikin wadanda aka kama akwai 42 da ake zargi da fashi da makami, 33 da ake zargi da garkuwa da mutane, 12 da laifin kisa.

Haka zalika akwai mutane 6 da aka kama bisa mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, biyar da laifin fyade, da 44 da ke cikin kungiyoyin asiri.

Sanda
An kama masu laifi da dama a jihar Enugu. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana cewa an ceto mutane 36 daga hannun masu garkuwa da mutane, tare da kwato bindigu 44, harsashi 173 da motoci 20.

Kwamishinan ya bukaci jama’a da su cigaba da ba da hadin kai da bayar da bayanai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

'Yan bindiga sun kai hari a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari wata kasuwa a karamar hukumar Wase.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun fara harbi a lokacin da ake tsaka da cin kasuwar kuma sun sace mutane.

Baya ga haka, wani mai sayar da kayayyaki a kasuwar ya bayyana cewa 'yan bindigar sun dauki abinci a kan babura sun tafi da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng