Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan Boko Haram bayan Musayar Wuta a Borno

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan Boko Haram bayan Musayar Wuta a Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi bata-kashi da tsagerun 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a jihar Borno
  • Sojojin sun samu nasarar fatattakar 'yan ta'addan bayan da suka yi yunkurin kawo wani hari a sansaninsu da ke yankin Kirawa
  • Bayan musayar wuta, sojojin sun hallaka 'yan ta'adda da dama tare da kwato makamai da sauran kayan aiki masu yawa daga hannunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun haɗin gwiwa na shiyyar Arewa-Gabas na rundunar Operation Hadi Kai, sun dakile wani harin 'yan ta'addan ISWAP/Boko Haram a Borno.

Dakarun sojojin sun dakile harin, inda suka kashe mayaka 12 a lokacin da aka yi musayar wuta a yankin Kirawa na jihar Borno.

Sojoji sun fatattaki 'yan ta'addan Boko Haram a Borno
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke tsohuwa mai taimakon 'yan ta'addan Boko Haram a Borno

Sojoji sun yi arangama da 'yan ta'adda

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare ranar 22 ga watan Mayu a lokacin gudanar da ayyukan tsaro na Operation Desert Sanity V da kuma Siege Operations da ake ci gaba da yi.

A cewar majiyoyin, ’yan ta’addan sun yi ƙoƙarin kutsa kai cikin mazaunin dakarun sojojin ne daga ɓangaren ƙasar Kamaru, amma aka hango su lokacin da suke matsowa kusa, inda aka yi musayar wuta mai zafi da su.

Dakarun sojojin, waɗanda aka ce suna cikin shirin ko-ta-kwana, sun mayar da martani cikin gaggawa ga harin, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa cikin fargaba.

'Yan ta'addan sun tarwatse inda suka koma tsallaken iyaka zuwa ƙasar Kamaru, inda aka ruwaito cewa da dama daga cikinsu sun samu raunukan harbin bindiga.

Majiyoyin sun ƙara da cewa an samu nasarar gudanar da aikin ne sakamakon tallafin tattara bayanan sirri, sa ido, gami da hare-haren dakarun sama da kuma haɗin gwiwa da abokan hulɗa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan bindiga sun sace mataimakiyar shugabar karamar hukuma

Sojoji sun yo barna ga 'yan Boko Haram

Binciken farko na tantance irin ɓarnar da aka yi a fagen fama ya nuna cewa an kashe ’yan ta’adda 12, yayin da adadin da ba a tantance ba suka sami raunuka a lokacin arangamar.

Majiyoyin sun bayyana cewa soja ɗaya ne ya samu rauni a lokacin fafutukar da aka yi a tsagerun 'yan ta'addan.

Ba a sami asarar kowane irin makami ko kayan aiki ba a ɓangaren dakarun sojin, yayin da aka samo abubuwa da dama a hannun ’yan ta’addan, waɗanda suka haɗa da bindigogi ƙirar AK-47, sassan makamin RPG, harsasai, da kuma wani kunshin kayayyaki daban-daban.

Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun cafke mai taimakon 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar cafke wata mata mai taimakon 'yan ta'adda a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun kama matar ne lokacin da suke gudanar da binciken tsaro na yau da kullum a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Majiyoyi sun bayyana cewa wadda ake zargin, an tare ta ne yayin da ake zarginta da kai wa ɗanta kayan abinci da sauran kayan buƙatu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng