'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Jam'iyyar APC, Sun Turo Saƙo ga Iyalansa
- Wasu ƴan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace shugaban APC na mazaɓa ta 5 a ƙaramar hukumar Ose da ke jihar Ondo
- Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun lakaɗa masa dukan tsiya kafin su tasa keyarsa zuwa cikin daji a daren ranar Litinin
- Rundunar ƴan sanda, mafarauta da sojoji sun bazama cikin dazuka domin ceto wanda aka sace cikin ƙoshin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Wasu mahara da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace Hon. Nelson Adepoyigi, shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Ose da ke jihar Ondo.
Hon. Nelson Adepoyigi, wanda shi ne shugaban APC a gunduma ta 5 watu Ifon a ƙaramar hukumar Ose ya faɗa hannun maharan ne da daren ranar Litinin a titin Benin-Ifon-Owo.

Asali: Original
Yadda aka sace shugaban APC a Ondo
A cewar rahoton Leadership, an sace Adepoyigi ne da misalin karfe 10 na dare ranar Litinin, lokacin da yake ajiye motarsa a cikin gidansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun farmaki gidan ne, inda suka yi masa dukan kawo wuka da sanda kafin su yi awon gaba da shi a cikin duhu.
Matarsa da ta ji ihunsa ta fito da gudu, amma kafin ta isa, tuni ƴan bindigar sun tafi da mijin na ta.
Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwar sun kira iyalan Hon. Adepoyigi kuma suna neman kudin fansa har Naira miliyan 100 kafin su sako shi.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Kwamandan dakarun Amotekun na Jihar Ondo, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’ansa sun fara bincike da sintiri domin ceto shugaban APC da aka ɗauke.
Haka zalika, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), Olushola Ayanlade, ya tabbatar da sace Adepoyigi a kofar gidan gonarsa da ke kan titin Ifon zuwa Owo.
Kakakin ƴan sandan ya kuma tabbatar da cewa tuni dakarun ƴan sanda suka fara farautar maharan domin kubutar da wanda aka sace da kuma cafke masu laifin.

Asali: Getty Images
Sojoji da ƴan sanda sun shiga dazuka
A rahoton da Daily Trust ta tattaro, mai magana da yawun ƴan sanda ya ce:
"Ina tabbatar da cewa an sace shugaban APC na mazaba ta 5 a kofar gidan gonarsa da ke kan titim Benin-Ifon-Owo.
"Bayan samun rahoton abin da ya faru, DPO na Ifon tare da mafarauta, jami’an rundunar VGN da Sojojin Najeriya sun shiga dazuka domin ceto wanda aka sace.”
Ayanlade ya buƙaci duk wanda ke da wani sahihim bayani ya garzaya ya sanar da ƴan sanda domin ceto shugaban APC cikin ƙoshin lafiya.
Ƴan bindiga sun sace masu ibada a Kogi
A wani labarin, mun kawo maku cewa ƴan bindiga sun kai farmaki kan jama'a suna tsaka da bautar Ubangiji a jihar Kogi.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi awon gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba daga cikin masu ibadar dare ta addinin kirista.
Ganau sun bayyana cewa ‘ yan bindigar sun shiga wurin ibadar su na harbi kan mai uwa da wabi domin tayar da hankula, kafin daga bisani su tafi da mutane.
Asali: Legit.ng