JAMB: Majalisa Ta Tattake Wuri kan 'Tangarɗa' da Aka Samu a Sakamakon UTME 2025
- Majalisar Wakilan Tarayya ta yanke shawarar gudanar da bincike kan yadda aka samu tangarɗa wurin fitar da sakamakon jarabawar UTME 2025
- Ta ɗauki wannan matsaya ne bayan amincewa da kudirin gaggawa da ɗan Majalisa daga jihar Osun, Adewale Adebayo ya gabatar yau Alhamis
- Tun farko hukumar shirya jarabawar share fagen shiga manyan makarantu ta tabbatar da cewa an samu tangarɗa a sakamakon na UTME 2025
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar Wakilai ta amince za ta gudanar da bincike kan kuskuren da aka samu wajen fitar da sakamakon jarabawar share fagen shiga manyan makarantu (UTME).
Hukumar shirya jarabawar watau JAMB ta fito fili ta tabbatar da cewa an samu tangarɗar na'ura wajen sakin sakamakon jarabawar UTME ta bana 2025.

Asali: Twitter
The Cable ta ce Majalisar Wakilai ta yanke shawarar gudanar da bincike kan kuskuren fasaha da ya lalata sakamakon jarabawar JAMB ta dubban ɗalibai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta cimma wannan matsaya ne a zamanta na ranar Alhamis, bayan da ta amince da wani kudurin gaggawa da dan majalisa daga jihar Osun, Adewale Adebayo, ya gabatar.
JAMB ta tabatar an samu kuskure a UTME
A ranar 9 ga Mayu 2025, JAMB ta saki sakamakon UTME, kuma alƙaluma suka nuna cewa aƙalla kashi 78% na ɗaliban da suka rubuta jarrabawar sun ci maki ƙasa da 200.
Wannan sakamako ya haifar da ce-ce-ku-ce da zarge-zarge daga al’umma kan ingancin tsarin jarrabawar gaba ɗaya.
Sai dai a taron manema labarai da ya kira a Abuja ranar Laraba, Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa an samu tangarɗar fasaha a sakamakon ɗalibai 379,997.
Majalisa ta tattake wuri kan sakamakon JAMB
Da yake gabatar da kudirin, Hon. Adebayo ya koka kan yadda ɗalibai suka sha wahala matuka wajen zuwa cibiyoyin zana jarabawar, ga kuma matasalar da aka samu.
A nasa jawabin, Hon. Sada Soli daga jihar Katsina ya bukaci majalisar da ta yaba wa shugaban JAMB bisa yadda ya fito fili ya amince da kuskuren da aka samu kuma ya nemi afuwar al’umma.
Ya ce Farfesa Oloyede ya nuna ƙwarin gwiwa da gaskiya tun bayan hawansa kujerar shugaban hukumar, kuma ya ƙara samar da kudin shiga a JAMB.

Asali: Twitter
Wane mataki Majalisar Wakilai ta ɗauka?
Sai dai Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya ce kwamitin da zai gudanar da bincike ne kawai ke da ikon yanke hukuncin yaba wa shugaban JAMB ko akasin hakan.
Majalisar ta amince da kudirin ne bayan mambobinta sun kada kuri'ar murya a zamansu na yau Alhamis, kamar yadda Channels tv ta kawo.
Daga ƙarshe, majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gina cibiyoyin CBT a kowanne karamar hukuma (LGA) a fadin ƙasar.
Majalisa ta yi watsi da tsarin karɓa-karɓa
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Wakilai ta ƙi amincewa da kudirin tsarin karɓa-karɓa a kujerar shugaban ƙasa da mataimakinsa.
Majalisar ta yi watsi da kudurin sauya kundin tsarin mulki wanda ya nemi a rika zagayawa da shugabancin ƙasa tsakanin yankuna shida.
Har ila yau, Majalisar Wakilan Tarayya ta yi fatali da wasu kudirori shida da suke nemi sauya dokokin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng