JAMB Ta Fitar da Sakamakon Jarabawar UTME 2025, Ta Rike Sakamakon Dalibai 39,834
- JAMB ta fitar da sakamakon UTME na 2025, amma ta riƙe sakamakon dalibai 39,834 saboda matsalolin da suka shafi kura-kuran jarrabawa
- Hukumar ta ce tana binciken mutane 80 da ake zargi da maguɗin jarrabawa, inda jihar Anambra ke da mafi yawan waɗanda ake zargi
- Shugaban JAMB, Is-haq Oloyede, ya bayyana cewa dalibai 467 da ba su kai shekaru 18 a sun samu maki kadan, amma 50 sun yi ba daidai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar shirya jarrabawar shiga jami'o'i (JAMB) a ranar Juma'a ta sanar da fitar da sakamakon jarrabawar shiga manyan makarantu (UTME) na shekarar 2025.
Wannan na nufin cewa daliban da suka rubuta jarrabawar UTME ta wannan shekarar za su iya fara duba sakamako tun daga safiyar ranar Juma'a.

Asali: Facebook
Ana bincikar masu magudin jarabawar JAMB
Jaridar Vanguard ta rahoto hukumar ta bayyana cewa ta riƙe da sakamakon jarabawar dalibai 39,834 saboda wasu matsaloli da suka shafi kura-kuran jarrabawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya nuna cewa sama da dalibai miliyan 1.9 ne suka zana wannan jarrabawar da aka kammala kwanan nan.
JAMB ta kuma bayyana cewa akwai dalibai 80 da ake bincikarsu a fadin kasar nan a halin yanzu saboda zarge-zargen maguɗin jarrabawa.
Hukumar ta yi nuni da cewa jihar Anambra ke kan gaba da mutane 14 da ake zargi da aikata laifuffuka daban daban na magudin.
An fitar da sakamakon jarabawar JAMB 2025
Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana haka ne a ranar Juma'a yayin da yake sanar da fitar da sakamakon UTME na 2025 a hukumance.
Ya kuma bayyana cewa yayin da dalibai 467 da ba su kai shekaru 18 ba suka samu kasa da makin da aka gindaya, 50 daga cikinsu sun aikata maguɗin jarabawar.
Kafin sanar da sakamakon, JAMB ta bayar da cikakken bayani kan yadda aka yi aikin jarrabawar, inda ta fitar da alkaluman jarabawar da suka jefa mutane a damuwa.
Alkaluman sun nuna cewa sama da dalibai miliyan 1.5 sun samu ƙasa da maki 200, wanda shi ne matsakaicin makin da ake karɓa don shiga jami'o'i a Najeriya.

Asali: UGC
Gwamnati ta kare faduwar dalibai a JAMB
Da yake mayar da martani kan wannan ƙididdiga, ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya ce an samu karancin maki ne saboda kokarin gwamnatina dakile maguɗin jarrabawa.
Jaridar Punch ta rahoto Dakta Alausa yana cewa:
“Yawan rashin nasara a jarrabawar shiga manyan makarantu ta 2025 shaida ce karara cewa matakan da gwamnati ta ɗauka na yaƙi da maguɗi suna aiki, musamman a bangaren JAMB.”
Ana tsammanin sakamakon UTME na 2025 zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance wadanda za su shiga manyan makarantu daban-daban a faɗin Najeriya.
Yadda ake duba sakamakon JAMB 2025
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, hukumar JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME na 2025, kuma ta bayyana hanyoyin duba makin da dalibai suka samu cikin sauki.
Hanya ta farko don duba sakamakon jarabawar ita ce ta hanyar tura sakon kar-ta-kwana (SMS); inda za a aika da kalmar "RESULT" zuwa 55019 ko 66019 ta lambar wayar da aka yi rajistar JAMB.
Wata hanyar da za ku iya ganin sakamakon JAMB ɗinku ita ce ta ziyartar shafin yanar gizon JAMB, inda dalibai za su sanya lambar rajista, sannan duba sakamakon.
Asali: Legit.ng