Zargin Ta'addanci: Mazauna Katsina Sun Taso Sarki a Gaba, Sun Roki Gwamna Radda

Zargin Ta'addanci: Mazauna Katsina Sun Taso Sarki a Gaba, Sun Roki Gwamna Radda

  • Mazauna garin Yanmaulu a Baure da ke jihar Katsina, sun nemi a dakatar da mai rikon sarautar yankinsu, Iliya Mantau
  • Sun ce Mantau ya shafe wata takwas a tsare kan sace Zulaihat Sidi da jaririnta, inda mijinta ya biya fansar N20m
  • Al’umma sun bukaci Gwamna Radda ya sa baki, su na gargadi cewa sakin Mantau zai dawo da matsalar tsaro a yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Baure, Katsina - An taso wani basarake a gaba a jihar Katsina kan zargin hannu a ayyukan 'yan bindiga.

Mazauna garin Yanmaulu da ke karamar hukumar Baure a jihar Katsina sun bukaci Gwamna Dikko Umaru Radda ya dakatar da mai rikon sarautar yankin, Iliya Mantau.

An taso Sarki a gaba a Katsina
An bukaci dakatar da Sarki a Katsina. Hoto: Dikko Umaru Radda.
Asali: Facebook

Zargin da ake yi wa Sarki a Katsina

Rahoton Thisday ya ce ana zargin Mantau da hannu cikin garkuwa da mutane da wasu laifuffukan da suka shafi aikata laifi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mantau, mai shekara 52, ya kwashe fiye da wata takwas a tsare saboda zargin sace Zulaihat Sidi da jaririnta mai wata uku.

Ana zargin ya sace ta ne a kauyen Angwan Rai da ke garin Yanmaulu a ranar 21 ga Oktobar 2022, inda aka ce yana taimakawa masu garkuwa da mutane da kuma ya boye su.

Mijin wadda aka sace da jaririnta, kamar yadda mazauna garin suka bayyana, ya biya N20m kafin a sako su daga hannun masu garkuwar bayan kwana takwas a tsare.

Wasu daga cikin mazauna garin da suka tattauna da ’yan jarida sun bukaci majalisar sarakunan Daura da ta dakatar da Mantau.

Mazaunan sun zargi wasu mutane daga fadar sarakunan Daura da hada kai da jami’an tsaro domin ganin an saki Mantau.

Sun ce dawowarsa za ta kara tabarbarewar tsaro a wannan yankin da ke da noman amfanin gona da kiwo.

Ana zargin Sarki da ta'addanci a Katsina
Zargin ta'addanci: An bukaci dakatar da Sarki a Katsina. Hoto: Legit.
Asali: Original

Katsina: An roƙi Gwamna Radda kan ta'addanci

Wani mazaunin garin, Mohammed Abdullahi ya ce an kama wasu mutum bakwai da ake zargin suna da hannu a cikin garkuwar, kuma sun tabbatar da cewa suna aiki tare da mai rikon sarautar.

Ya ce:

“Tun bayan kama Iliya Mantau da wasu mutum bakwai da ake zargi da sace Zulaihat Sidi da jaririnta, babu wani rahoton garkuwa da mutane a wannan gari da kewaye.
"Don haka muna bukatar a dakatar da Iliya Mantau daga matsayin mai rikon sarautar Yanmaulu.
“Muna kira ga Gwamna Dikko Umaru Radda da ya sa baki cikin wannan lamari. Muna rokon jami’an tsaro kada su saki Mantau saboda dawowarsa zai kawo matsalar tsaro.”

An ƙona fadar Sarki a Katsina

Kun ji cewa wasu matasa a garin Tsiga a jihar Katsina sun kone fadar dagacin garin bayan wani barawo ya nemi mafaka.

Jama’a sun bukaci a mika musu ɓarawon babur din amma aka hana, lamarin da ya tayar da hankali har ya kai ga kona fadar.

An ce wanda aka daba wa wuka yanzu yana cikin mawuyacin hali, yayin da lamarin ke kara tayar da kura a yankin karamar hukumar Bakori.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.