An Kuma: Aƙalla Shanu 18 Suka Mutu bayan Cin Guba a Wata Gona a Plateau

An Kuma: Aƙalla Shanu 18 Suka Mutu bayan Cin Guba a Wata Gona a Plateau

  • Akalla shanu 18 sun mutu bayan sun yi kiwo a gonar da aka zuba magani a kauyen Vwei, karamar hukumar Riyom, Jihar Plateau
  • Bayanai daga mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:00 na rana a ranar Laraba 30 ga watan Afrilun 2025
  • An tabbatar cewa shanu bakwai aka yanka saboda cin amfanin gona mai guba, yayin da wasu 11 suka mutu nan take a cikin gonar da aka zuba maganin
  • Ana kula da sauran shanu 15 da suka kamu da cuta bayan maganin da aka shafa a gonar, a cewar wata majiya daga yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Riyom, Plateau - Rahotanni sun tabbatar da cewa an sake samun gawarwakin wasu shanu da suka shiga gona a Plateau.

An ce akalla shanu 18 ne suka mutu bayan da suka ci ciyawa a wata gona da aka zuba magani.

An yi asarar shanu masu yawan bayan cin guba a gona
Wasu shanu 18 sun gamu da ajalinsu bayan cin guba a gona da ke Plateau. Hoto: Legit.
Asali: Original

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a kauyen Vwei da ke Riyom a Plateau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An hallaka wasu shanu a jihar Plateau

Hakan ya biyo bayan hallaka wasu shanu na Fulani a ƙaramar hukumar Riyom da ke jihar Plateau.

An ce wasu mutane da ba a san ko su wane ba sun harbe shanu 37 a yankin Tashek a ƙaramar hukumar Riyom a jihar Plateau, kamar yadda MACBAN ta bayyana.

Wannan hari na zuwa ne mako guda bayan makamancin haka a unguwar Tanjol inda makiyaya biyu suka jikkata kuma aka kashe shanu guda biyar.

Shugaban MACBAN na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya ce an sanar da hukumomin tsaro kuma ana jiran matakin da za su ɗauka kan lamarin.

Wasu shanu sun mutu saboda guba a Plateau

Wannan ba shi ne karon farko ba da ake samun mutuwar dabbobi a jihar Plateau da ke Arewacin Najeriya.

Sojojin Operation Safe Haven (OPSH) sun gaggauta kai dauki bayan bullar rahoton sanya wa shanu 32 guba a yankin karamar hukumar Bassa da ke Jihar Plateau.

Rahotanni sun ce shanun mallakin wani makiyayi mai suna Samaila Nuhu ne, inda suka mutu bayan sun ci abinci a wani fili a tsakanin Dutsen Kura da Jebbu Miango.

Shanu sun mutu bayan cin guba a Plateau
Rahotanni sun ce shanu aƙalla 18 suka mutu bayan cin guba a Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang, @ZagazOlamakama.
Asali: Facebook

Yadda aka yi asarar shanu a Plateau

A cewar wata majiya daga yankin, lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:00 na rana a ranar Laraba, lokacin da shanun suka shiga gonar.

Wata majiya ta ce:

“An yanka shanu bakwai saboda sun kamu da cuta daga maganin, yayin da wasu 11 suka mutu nan take.

Majiyar ta ƙara da cewa wasu shanu 15 da suka jikkata saboda maganin da aka shafa a gonar yanzu haka ana basu kulawa.

Wani Fulani makiyayi ya yi magana da Legit Hausa

Sambo Adamu da ke yankin Kwami a jihar Gombe ya ce ya kamata jami'an tsaro su yi bincike sosai kan abin da ya faru.

Ya ce:

"Ba mu goyon bayan shanu su rika barna amma tabbas akwai abubuwa da ke faruwa da jama'a ba su sani."

Ya ce babu wanda yake son tashin hankali amma ya shawarci manoma da makiyaya su zauna lafiya da juna.

Sheikh Jingir ya jajanta iftila'in gobara

Kun ji cewa shugaban Majalisar malamai a kungiyar Izalah, Muhammad Sani Yahya Jingir ya nuna alhini kan gobarar da ta tashi a kasuwar Taminus da ke Jos.

Shehin ya yi addu’ar Allah SWT ya kiyaye gaba, sannan ya roƙi gwamnati da masu hannu da shuni su tallafa wa waɗanda suka yi asara.

Sheikh Jingir ya buƙaci hukumar kashe gobara ta duba matsalolinta tare da gyara domin a guji sake fuskantar irin wannan masifar nan gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.