'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Wata Makarantar Zamfara, an Tafka Barna

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Wata Makarantar Zamfara, an Tafka Barna

  • An shiga jimami a jihar Zamfara bayan wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a wata makarantar sakandiren gwamnati da ke Tsafe
  • Miyagun ƴan bindiga sun hallaka wani tsohon malamin makaranta bayan ya ƙi yarda su yi awon gaba da shi zuwa cikin daji
  • Ƴan bindigan sun kuma sace wasu mata da ke zaune a gidajen malamai na makarantar wacce take ta jeka ka dawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun kashe wani tsohon malamin makarantar sakandare tare da sace mata uku a wani hari da suka kai a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun kai harin ne da daddare a gidan malamai na makarantar sakandiren gwamnati da ke Tsafe, a jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun kashe tsohon malamin makaranta a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Zamfara

Tashar Channels tv ta ce tsohon malamin da aka kashen wanda aka bayyana sunansa a matsayin Mallam Kabiru, ya rasa ransa ne lokacin da ƴan bindigan suka harbe shi bayan ya ƙi yarda a sace shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar marigayin da wasu mata biyu waɗanda ke zaune a gidan malamai da ke makarantar an yi awon gaba da su, rahoton jaridar TheCable.

Ƴan sanda sun tabbatar da harin

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin

A cewar DSP Yazid Abubakar, ƴan bindigar sun kai harin ne da dare a ranar Asabar, 10 ga watan Mayun 2025.

Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun shiga cikin makarantar ne bayan sun fasa katangarta.

“An tabbatar da cewa lamarin ya faru da dare kusan ƙarfe 10:00 na dare. Makarantar jeka ka dawo ta gwamnati ce, don haka babu ɗalibai a cikin makarantar a lokacin da aka kai harin."
“Sun shigo ta wajen gidajen malamai, suka fasa katanga, suka shiga har cikin harabar makarantar, sannan suka kashe Malam Kabir Abdullah, wanda ya riga ya yi ritaya."
“Shi tsohon malami ne. Ya ƙi yarda a tafi da shi, sai suka harbe shi har lahira. Mata uku aka sace, ciki har da matar tsohon malamin."

“’Yan sandanmu suna can a wurin domin tabbatar da tsaro, kuma muna kan aiki don ceto waɗanda aka sace.”

- DSP Yazid Abubakar

'Yan bindiga sun kashe malami a Zamfara
'Yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wannan sabon hari ya sake bayyana yadda matsalar tsaro ke ƙara tabarbarewa a jihar, da kuma yadda fargaba ke ƙara yaduwa a cikin al’ummomi da dama a Arewacin Najeriya.

Hare-haren ƴan bindiga dai sun kusa zama ruwan dare a wasu sassan jihar Zamfara wacce ta daɗe tana fama da rashin tsaro.

Ƴan bindiga sun hallaka basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai wani harin ta'addanci a jihar Benue.

Miyagun ƴan bindigan sun hallaka Chief Anthony Adejoh wanda shi ne Hakimin ƙauyen Odugbeho da ke ƙaramar hukumar Agatu ta jihar.

Ƴan bindigan sun hallaka basaraken ne tare da wani mai suna Jerry John a ranar Laraba, 7 ga watan Mayun 2025 lokacin da suke tsaka da gudanar da aiki a gona.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng