Neja: An Rufe Gidan Karuwai da Gidajen Giya a Kusa da Masallacin Juma'a
- Hukumar bayar da lasisin giya a Jihar Neja ta rufe otel da ke da ɗakuna 50 tare da gidajen giya 13 da ke kusa da babban masallacin Juma’a a Mokwa
- Rahotanni sun bayyana cewa otel ɗin na cike da karuwai, kuma yana kawo cikas ga zaman lafiya da ayyukan addini a yankin da ya ke ƙaramar hukumar
- An gudanar da wannan aiki ne a karkashin jagorancin hukumar lura da sayar da giya domin kawar da gidajen giya da ke aiki ba bisa ƙa’ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Gwamnatin Neja ta dauki sabon mataki domin dakile yaɗuwar aikata laifuffuka da ɓata tarbiyya, inda ta rufe otel da aka ce cike yake da karuwai tare da wasu gidajen giya.
Otel ɗin da aka rufe yana kusa da babban masallacin Juma’a da ke Mokwa, wanda mazauna yankin suka dade suna kuka da shi bisa dalilin kawo cikas ga ayyukan addini.

Asali: Twitter
Punch ta wallafa cewa an gano gidajen giya da dama da ke yankunan Mokwa, Lavun da Edati ba su da lasisin aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan mataki ya zo ne yayin da hukumar kula da lasisin giya a jihar ke rangadi na musamman domin ganin an dakile ayyukan da suka sabawa doka.
An rufe gidan karuwai da ke kusa da masallaci
Binciken hukumar ya nuna cewa otel ɗin da ke kusa da masallacin Mokwa yana da ɗakuna 50, kuma dukkansu cike suke da karuwai.
Lamarin ya janyo matsaloli ga mazauna da masu ibada a yankin, inda ake yawan korafi kan hayaniya da ɓarna da ke fitowa daga wajen.
Wani jami’in hukumar, Mohammed Hamisu, ya bayyana cewa sun tuntuɓi mai otel ɗin, wanda tsohon kansila ne a Bitagi, kuma ya yarda ya dakatar da harkar da yake yi.
Ya ce tsohon kansilan ya nuna shirin sayar da wajen ga wanda zai gina Islamiyya ko faɗaɗa masallaci.
An rufe gidajen giya kusa da masallaci
Hukumar ta ce yawancin gidajen giyan da aka rufe na aiki ne ba tare da lasisi ba ko kuma suna cikin yankuna da aka haramta sayar da giya.
Rahoton Daily Post ya nuna cewa hukumar ta ce hakan ya sabawa dokokinta, kuma ya janyo rufe su kai tsaye.

Asali: Facebook
Yahaya Halidu ne ya bayar da umarnin a gudanar da binciken da kuma kulle wuraren, inda suka gano cewa yawancin masu shaye-shaye da masu aikata ba daidai ba na fakewa a can.
Zuwan gwamnan Neja coci ya jawo magana
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Neja ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya ziyarci wani coci a jihar.
An ruwaito cewa gwamnan ya yi wasu maganganu da mutane suka ce ba su dace ba yayin da ya kai ziyarar.
Sai dai duk da korafin da mutane suka yi, gwamnan jihar bai yi magana da ke nuna martani ne game da abin da aka fada ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng