A Karshe, Dangote Ya Fadi Masu Kokarin Durkusar da Matatarsa da ke Legas

A Karshe, Dangote Ya Fadi Masu Kokarin Durkusar da Matatarsa da ke Legas

  • Aliko Dangote ya bayyana cewa manyan 'yan kasuwar fetur ne ke kokarin hana nasarar matatarsa, ba shugabannin NNPCL ba
  • Ya jinjinawa Bola Tinubu bisa nada kwararru a matsayin shugabannin kamfanin NNPC, yana mai cewa za su kawo sauyi mai amfani
  • Dangote ya ce shugabannin sun nuna cikakken goyon baya ga matatar shi, kuma suna aiki da irin hangen nesa na shugaba Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana wadanda ke kokarin kawo cikas ga ci gaban matatar shi.

Alhaji Aliko Dangote ya wanke sababbin shugabannin NNPCL daga zargi, yana cewa manyan 'yan kasuwar mai ne suka saka shi a gaba.

Dangote
Dangote ya ce 'yan kasuwa ne ke kokarin durkusar da matatarsa. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Punch ta wallafa cewa Dangote ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce sababbin shugabannin NNPCL na aiki da gaskiya da hangen nesa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kai ziyara ga Bola Tinubu domin gode masa bisa zabar kwararrun mutane da za su taimaka wajen inganta NNPCL da kuma harkar man fetur gaba daya a Najeriya.

Dangote ya jinjinawa shugabannin NNPCL

A cewar Dangote, sabon kwamitin jagoranci na NNPCL ya kunshi kwararru a fannin fasaha da shugabanci, wadanda za su taimaka wajen farfado da kamfanin.

Nairametrics ta rahoto cewa Dangote ya ce:

“Mun gamsu cewa wannan sabon rukuni zai magance matsalolin da suka dade suna damun bangaren mai, tare da bin hangen nesan Shugaba Tinubu.”

Dangote ya kara da cewa sababbin shugabannin NNPCL na aiki da gaskiya da hangen nesa, kuma suna daukar matakan da za su sa a samu sauyi a harkar mai da iskar gas.

Ya ce kamfaninsa yana da cikakken tabbaci cewa karkashin wadannan shugabanni, Najeriya za ta kai ga babban matsayi a fannin makamashi.

Dangote
Dangote ya yabawa Tinubu kan sauye sauye a NNPCL. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Su wanene masu son durkusar da matatar Dangote?

Game da rahotannin da ke cewa har yanzu yana fafutukar ganin matatar mansa ta tsira daga cikas, Dangote ya ce wadannan kalaman nasa ba su shafi sababbin shugabannin NNPC ba.

Ya bayyana cewa:

“Wadanda nake nufi da suna kokarin takura aikin matatar su ne wasu manyan ‘yan kasuwa da ke kokarin hana ci gaban da gwamnatin Tinubu ke kokarin kawowa.”

Dangote ya jaddada cewa shugabannin NNPC sun riga sun nuna goyon bayansu ga kamfaninsa, kuma suna da niyyar yin gaskiya da rikon amana a fannin man fetur na Najeriya.

Ya kuma tabbatar da cewa kamfanin Dangote zai ci gaba da mara baya ga kokarin tabbatar da ci gaban Najeriya da wadatuwar makamashi.

Dangote ya ce zai yi nasara kan makiyansa

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya ce yana da tabbacin cewa zai yi nasara a kan wadanda suka saka shi a gaba game da matatar man shi.

Dangote ya bayyana haka ne yayin wani taron masu zuba jari a jihar Legas, inda ya ce ya shafe shekaru yana cin nasara kan kalubalen rayuwa.

Legit ta rahoto cewa Aliko Dangote ya ce masu son ganin bayan matatar da ya gina a Legas ba za su yi nasara a kan shi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng