Najeriya na Bukatar Sojoji Su Ƙwace Mulki a Halin Yanzu? Yakubu Gowon Ya Yi Bayani

Najeriya na Bukatar Sojoji Su Ƙwace Mulki a Halin Yanzu? Yakubu Gowon Ya Yi Bayani

  • Janar Yakubu Gowon (Mai ritaya) ya ce duk da halin da ake ciki a Najeriya, babu bukatar sojoji su karɓi ragamar mulki
  • Tsohon shugaban ƙasar na mulkin soji ya ce kamata ya yi dakarun sojoji su ci gaba da goyon bayan tsarin demokuraɗiyya har ta zauna da kafarta
  • Gowon ya kuma kawo mafita ga matsalar tsaron da ta addabi ƙasar nan, yana mai cewa sojoji na bukatar kayan aiki na zamani da kayan leƙen asiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya bayyana cewa duk da cewa akwai kura-kurai a tsarin dimokuraɗiyya, bai kamata Najeriya ta sake komawa mulkin soja ba.

Gowon ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, yayin kaddamar da wani littafi mai suna “Mulkin soji a tarihin Najeriya 1960–2018."

Yakubu Gowon.
Yakubu Gowon ya ce Najeriya ba ta buƙatar sojoji su karɓi mulki a yanzu Hoto: Yakubu Gowon
Asali: Facebook

Vanguard ta tattaro cewa Ƙungiyar Tarihi ta Najeriya (HSN) ce ta wallafa wannan littafi a matsayin wani bangare na bikin cikarta shekara 70 da kafuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya na bukatar sojoji su karɓi mulki?

Da yake jawabi, Yakubu Gowon ya ce duk da gudunmawar da mulkin soji ya bayar wajen samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a Najeriya, ya kamata sojoji su ci gaba da goyon bayan tsarin dimokuraɗiyya.

“Zamanin mulkin soja ya wuce, ya zama tarihi. Duk da halin da dimokuraɗiyya ke ciki a yanzu, ita ce hanya mafi dacewa wajen samar da ci gaban kasa da shigar jama’a cikin harkokin mulki.”

- Yakubu Gowon.

Ya ce dole ne rundunar soji ta rungumi aikinta na kare iyakokin ƙasa bisa kundin tsarin mulki, ba shiga harkokin siyasa ko mulki ba, Daily Trust ta rahoto.

Wace gudummuwa sojoji suka ba Najeriya?

Gowon, wanda shi ne shugaban taron, ya ce gudummuwar da sojoji suka taka bayar a tarihin Najeriya ba labarin jarumta ba ne kawai, wani tarihi ne mai muhimmanci a ƙasar nan.

Ya bayyana cewa a yanzu tambayar ko mulkin da sojoji suka yi ya taimaka ko cutar da Najeriya na daga cikin abubuwan da ake ta muhawara a kai.

“A wannan lokaci da shekaruna suka ja, ina ganin amsar tana tsakanin biyun. Sojoji sun kare hadin kan kasa lokacin yakin basasa, sun gina ababen more rayuwa, sun kirkiro jihohi domin kusantar da gwamnati ga jama’a."
Yakubu Gowon.
Yakubu Gowon ya buƙaci a samar da kayan aiki na zamani ga sojoji Hoto: Yakubu Gowon
Asali: Getty Images

Yakubu Gowon ya ba da shawara kan tsaro

Game da matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta a yanzu, Gowon ya ce akwai bukatar rundunar soji ta samu kayan aiki na zamani kuma ta inganta harkokin tattara bayanan sirri.

Haka kuma, ya bukaci a hada karfi da karfe tsakanin rundunar soji da sauran hukumomin tsaro da al’umma gaba daya domin dawo da zaman lafiya.

Mulkin soji da dimokradiyya a Najeriya

Mulkin soja a Najeriya ya kasance lokaci ne da aka samu tsari mai ƙarfi wajen shugabanci, musamman wajen tabbatar da tsaro da kuma samar da ababen more rayuwa.

Sojoji sun taka muhimmiyar rawa wajen kare haɗin kai a lokacin rikicin basasa, wanda ya ba da damar ci gaban tattalin arziki a wasu fannoni.

Sai dai kuma, mulkin soja ya zo da kalubale na rashin yanci ga talakawa, da kuma rashin shigar jama’a cikin harkokin mulki.

A gefe guda kuma, tsarin dimokuraɗiyya yana ba jama’a damar zabar shugabanninsu kai tsaye da kuma samun damar shiga cikin yanke shawara a matakai daban-daban na gwamnati.

Duk da matsalolin cin hanci, rashin tsaro da ƙalubalen shugabanci, dimokuraɗiyya na bai wa Najeriya damar samun ingantaccen tsarin mulki da ake ci gaba da gyarawa.

Idan aka duba, dimokuraɗiyya ce hanyar da ta fi dacewa wajen tabbatar da ci gaba da zaman lafiya da shigar jama’a cikin mulki.

Mulkin soja ya yi tasiri mai kyau a lokacin da aka fi bukatar tsaro, amma dimokuraɗiyya na samar da yanayi mai kyau na shugabanci na gaskiya da kiyaye haƙƙin ɗan adam.

Saboda haka, Najeriya za ta ci gaba da buƙatar tsarin dimokuraɗiyya mai ƙarfi tare da inganta rundunar tsaro.

Sule Lamido ya taɓo batun MKO Abiola

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya buƙaci Shugaba Tinubu ya biya MKO Abiola ya biyo gwamnatin Najeriya.

Sule Lamido ya yi wannan kiran ne a Abuja a ranar Talata, yayin da ake ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa.

Ya ce biyan bashin zai taimaka wajen rufe cece-kuce da rikicin da ke tattare da zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yuni, 1993, wanda Abiola ya samu nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262