Zargin Zamba: An Yi Zanga Zangar Neman Dawo da Tsohon Shugaban NNPCL Najeriya
- Wasu ‘yan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofisoshin jakadancin Najeriya da Birtaniya kan tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari
- Sun yi zargin cewa Kyari ya tsere daga Najeriya domin kaucewa fuskantar shari’a kan almundahana da wawurar kudin kamfanin man fetur
- Kungiyar ta bukaci hukumomin Birtaniya da kada su ba Kyari kariya don hakan zai kawi tarnaki ga yaki da cin hanci da rashawa da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Wasu ‘yan Najeriya karkashin wata kungiya mai suna Rescue Nigeria Now sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Najeriya da na Birtaniya.
Sun mika bukatarsu na cewa lallai a dawo da tsohon shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL), Mele Kyari, gida Najeriya domin fuskantar tuhuma.

Asali: Facebook
The Cable ta ruwaito cewa masu zanga-zangar sun rike alluna masu dauke da rubuce-rubuce irin su: "A soke zaman Mele Kyari a Birtaniya yanzu!", da "Mele Kyari koma gida ka fuskanci EFCC yanzu!"
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin Kyari da almundahana a NNPCL
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kungiyar na zargin Mele Kyari da tserewa daga Najeriya domin kaucewa fuskantar shari’a kan zargin aikata almundahana da wawurar dukiyar kasa.
A wata wasika da kungiyar ta aikewa da jakadan Najeriya a Birtaniya, Sarafa Tunji Isola, sun bayyana cewa kasancewar Kyari a kasar cin fuska ne ga yaki da rashawa.
Kungiyar ta ce:
“Muna bukatar ofishin jakadancin Najeriya da ke Birtaniya da kada ya bai wa Mele Kyari kowanne irin tarbar girmamawa ko daukar sa a matsayin wakili har sai ya koma Najeriya ya mika kansa ga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da sauran hukumomin bincike don fuskantar tuhumomin da ake masa.”
Ana son Mele Kyari ya fuskanci EFCC
Kungiyar ta kara da cewa yana da matukar muhimmanci Kyari ya fuskanci hukunci saboda abubuwan da ya aikata, kuma a dawo da duk wani kudin kasa da ake zargin an wawura.

Asali: Getty Images
Ta kara da cewa:
“Kungiyar ta bukaci hukumomin Birtaniya da su bi yarjejeniyar kasa da kasa da suka kulla da Najeriya don hana ayyuksan cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da cewa masu aikata laifuka ba su samu mafaka a kasashen waje ba.”
Kyari ya magantu kan zargin almundahana
A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari, ya ce duk ayyukan da ya gudanar a lokacin da yake shugabantar kamfanin ya yi su ne bisa tsoron Allah da gaskiya.
Tun bayan sauyin shugabanci da aka yi a kamfanin NNPCL, ana ta yada rahotanni daban-daban da ke nuna ana gudanar da bincike kan ayyukan Kyari da mutanen da suka yi aiki ƙarƙashinsa.
A cewar rahoton da jaridu suka wallafa, an gano naira biliyan 80 a asusun ɗaya daga cikin tsofaffin daraktocin matatar mai, wanda ya yi aiki a lokacin shugabancin Kyari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng