'Yan Bindiga Sun Yi Ta'adi, An Gano Gawar Ɗan Majalisar da Suka Sace a Wani Yanayi

'Yan Bindiga Sun Yi Ta'adi, An Gano Gawar Ɗan Majalisar da Suka Sace a Wani Yanayi

  • Ƴan bindiga sun kashe ɗan Majalisar dokokin jihar Anambra, Hon. Justice Azuka bayan sun sace shi a watan Disambar, 2024
  • Jami'an tsaron haɗin guiwa da ke bincike kan lamarin sun gano gawar marigayi ɗan Majalisar a gadar Neja ta 2
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Anambra, SP Tochukwu Ikenga ya ce sun tura dakaru domin su ɗauko gawar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - An gano gawar ɗaya daga cikin ‘yan Majalisar dokokin Jihar Anambra, Justice Azuka, a gadar Neja ta biyu kusan watanni biyu bayan sace shi.

Wata tawagar jami'an tsaron haɗin guiwa ne suka gano gawar ɗan majalisar, wanda aka jima ana nema bayan ƴan bindiga sun yi awon gaba da shi.

Justice Azuka.
Yan bindiga sun kashe dan Majalisa, an gano gawarsa a jihar Anambra Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Channels tv ta tattaro cewa mahara sun yi garkuwa da Justice Azuka, wanda ke wakiltar mazaɓar Onitsha ta Arewa 1, tun ranar 24 ga Disamba, 2024.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi tsaurin ido, sun yi garkuwa da Birgediya Janar Maharazu Tsiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka sace ɗan Majalisa

Ƴan ta'addan sun tare ɗan Majalisar ne a kan titin Ugwunabankpa da ke Inland Town a Onitsha.

Bayan makonni ana bincike, jami’an tsaron da aka turo daga Abuja sun cafke wasu da ake zargi da hannu a sace shi a daren Laraba.

Bugu da ƙari, wadanda aka kama ne suka jagoranci dakarun zuwa wurin da suka jefar da gawar ɗan majalisar wadda aka ce ta ma fara ruɓewa saboda daɗewa.

Jami'an tsaro sun gano gawar Azuka

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta bayyana cewa har yanzu ba a samu cikakken bayani kan lamarin ba, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Amma jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da cewa an tura jami’an tsaro zuwa wurin da aka gano gawar.

"Jami'anmu sun tafi ɗauko gawar kuma ina tunanin yanzu haka sun kusa dawowa nan hedkwatar ƴan sanda. Za mu fitar da sanarwa bayan an kawo gawar," in ji Ikenga.

Kara karanta wannan

Sarki ya jawo wa kansa wahala, an tasa ƙeyar mai martaba zuwa gidan gyaran hali

Wannan shi ne karo na biyu da aka yi garkuwa tare da kashe wani ɗan majalisar dokokin Anambra a cikin ‘yan shekarun nan.

A shekarar 2022, ƴan bindiga suka sace Okey Okoye, wanda aka fi sani da “Okey Di Ok” mai wakiltar Aguata, sannan aka yanke masa kai.

Bayan haka, jami'an tsaro sun gano gawarsa a yankin Nnobi da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Jami'an tsaro sun ragargaji miyagu a Anambra

Kun ji cewa jami'an tsaro na rundunar Agunechemba ta jihar Anambra tare da haɗin guiwar sojoji sun kai samame maɓoya ƴan bindiga.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan gwabzawa da ƴan ta'addan, dakarun tsaron sun yi nasarar hallaka da dama daga cikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262