'Yan Bindiga Sun Nunawa Gwamna Tsaurin Ido bayan Ya Kaddamar da Rundunar Tsaro
- Yan bindiga sun yi garkuwa da likitan kwakwalwa, Dr. Collinus Onuigbo wanda ke aiki a asibitin koyarwa na jam'ar Nnamdi Azikwe watau NAUTH
- Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun aikata wannan ta'adi ne kwanaki kaɗan bayan Gwamna Soludo ya kaddamar da rundunar Operaration Tsaro Dole
- Kakakin ƴan sandan Anambra, SP Tochukwu Ikenga ya ce sun samu labarin abin da ya faru kuma tuni dakaru suka fara farautar maharan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Wasu ‘yan bindiga da ba a gano ko su wanene ba sun sace ƙwararren likita da ke aiki a asibitin koyarwa na jami’ar Nnamdi Azikiwe (NAUTH), da ke Nnewi a jihar Anambra.
Lamarin ya faru ne kwanaki uku kacal bayan da Gwamna Chukwuma Soludo ya kaddamar da rundunar tsaro a ƙarƙashin shirin Operation Udo ga-achị, ma’ana “Dole ne zaman lafiya ya tabbata."

Asali: Facebook
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Gwamna Soludo ya kaddamar da rundunar tsaron ne a wani mataki na yaki da miyagun laifuka da kuma dawo da tsaro mai ɗorewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa wanda aka sace likitan kwakwalwa ne a asibitin NAUTH da ke Anambra a Kudu maso Gabashin Najeriya.
'Yan bindiga sun nuna tsaurin ido
Miyagun ƴan bindigar sun yi garkuwa da likitan mai suna Dr. Collinus Onuigbo, a daren jiya Talata, a gaban gidansa da ke kusa da asibitin koyarwa.
An ruwaito cewa tun bayan aukuwar lamarin, iyalan likitan ke ƙoƙarin ceto ɗan uwansu cikin ƙoshin lafiya amma dai har yanzu ba wani labari.
Lamarin dai ya jefa ƴan uwa da abokan arzikin likitan cikin tashin hankali duk da fara ɗaukar matakai da nufin ganin ya dawo gida lami lafiya.
Ƴan sanda sun tabbatar da sace likita
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa, Punch ta ruwaito.
Ya ce rundunar ƴan sanda tana kan bincike kuma ta baza dakaru su fara aikin ceto wanda aka sace ba tare da miyagun sun cutar da shi ba.
Kakakin ƴan sandan ya ƙara ɗa cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Anambra, Nnaghe Obono-Itam, ya bayar da umarnin gaggawa na ceto likitan da cafke miyagun.
Jami'an tsaro sun fara farautar ƴan binidga
SP Tochukwu Okenga ya ce dakarun ƴan sanda sun samu labarin abin da ya faru a kan lokaci kuma tuni suka kaddamar da aikin farautar waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.
Ya ce dakaru sun fara bin sahihan bayanan da suka samu da nufin cimma nasarar kama ƴan ta'addan da kuma ceto likitan asibitin NAUTH.
Yan sanda da sojoji sun gwaza da ƴan IPOB
A wani labarin, kun ji cewa dakarun ƴan sanda da sojoji sun sheƙe ƴan ta'addan IPOB da suka kai samame wani sansaninsu a jihar Anambra.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: Matasa sun yi tara tara, sun kama malamai 2 da wasu abubuwan ban mamaki
Dakarun sun kuma yi nasarar kwato miyagun makamai daga yan tada ƙayar bayan waɗan ke ikirarin fafutukar neman raba Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng