Abin da Sarki Sanusi III Ya Nemawa Kano a Taron Tattalin Arzikin Afrika a Tunisiya
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bukaci 'yan kasuwa na kasashen waje su zuba jari a Najeriya, inda ya ce akwai arziki a kasar
- Ya jaddada cewa akwai damammakin zuba jari a fannoni da dama kamar noma, masana’antu, fasahar sadarwa da kuma kirkire-kirkire
- Sarkin ya ce Kano na da albarkatu da damar kasuwanci, tare da ba da tabbacin duk wanda ya zuba arzikinsa a jihar zai kwashi riba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci 'yan kasuwa na kasashen waje da su ribaci arzikin Najeriya wajen zuba hannun jarinsu domin samun riba mai yawa.
Ya nemi haka a jawabinsa ga masu zuba jari na duniya da shugabannin masana'antu a taron Tattaunawar Zuba Jari da Kasuwanci na Duniya da ke gudana a Tunisiya.

Asali: Facebook
Arise News ta ruwaito cewa jawabin da Khalifa Sanusi ya yi na kunshe a sanarwa da Munir Sanusi Bayero, Galadiman Kano kuma babban mai taimakawa Sarki, ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Khalifa Muhammadu Sanusi II ya bayar da tabbacin cewa akwai duk abin da yan kasuwa suke bukata na zuba hannun jari a Najeriya da zummar samun riba.
'Ku zuba hannun jari a Najeriya,' Sarki Sanusi II
Primetimes ta ruwaito cewa tsohon Gwamnan Bankin CBN, ya bayyana cewa Najeriya tana daga cikin kasashen masu tattalin arziki mafi saurin girma a Afrika.
Sanarwar ta ce:
"Sanusi IIya yi kira ga manyan 'yan kasuwa da masu zuba jari da su amfana daga wannan tattalin arziki mai karfi da yanayin da zai ba su damar haɓaka jarinsu a fannonin Masana'antu, Noma, fasahar sadarwa, Kirkira da kuma bangaren kudi."
Ya shawarci yan kasuwar da kar su yi wasa da damar zuba jari a jihar Kano, wanda zai kawo wa jihar da ma yan kasuwar riba mai yawa.
Sarki Sanusi II ya tallata Kano a Tunisiya
Sarkin Kano ya tabbatar da cewa jiharsa tana da dukkanin albarkatun da ake bukata wajen zuba hannun jari da samun arziki.
Ya bayyana cewa Kano wuri ne na kasuwanci, harkokin ciniki da masana'antu da ke da yawan jama'a miliyan 22.

Asali: Facebook
Khalifa Sanusi II ya kuma ce akwai albarkatun kasa a Kano, wanda ke da muhimmanci ga ci gaban kasuwanci.
Ya shaidawa taron manyan yan kasuwa daga sassa daban-daban na duniya cewa Kano wuri ne da za su ci ribar sanya kudinsu domin kasuwanci.
Sarki Sanusi II ya halarci taro a Tunisiya
A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II, ya isa kasar Tunisia domin halartar babban taron kasa da kasa na tattalin arziki da ciniki da ake kira FITA2025.
Rahotanni sun ce wannan ziyara na daya daga cikin kokarin Sarki Sanusi na tallata damammakin zuba jari a jihar Kano da Najeriya baki daya, tare da jawo hankalin yan kasuwa.
An shirya taron FITA2025 ne karkashin kungiyar Tunisia Africa Business Council (TABC), wadda ke bikin cika shekaru 10 da kafuwa, kana wannan shi ne zagayen taron karo na takwas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng