Gwamnatin Kano Ta Yi Martani kan Cece Kucen Kashewa Masarauta N670m a Motoci

Gwamnatin Kano Ta Yi Martani kan Cece Kucen Kashewa Masarauta N670m a Motoci

  • Gwamnatin Kano ta kare kanta kan N670m da aka ware don gyara da sayen motocin Sarki Khalifa Muhammadu Sanusi II, ta ce hakan daidai ne
  • Kwamishinan yada labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce gwamnatin jiha na da alhakin kula da sarakuna, ciki har da saya masu motoci
  • An bayyana cewa a lokacin Mallam Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje ma an sayawa sarakuna sababbin motoci ba tare da cece-kuce ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi martani kan cece-kucen da ya barke, musamman a shafukan sada zumunta, kan saye da gyaran motocin Sarkin Kano.

A makon da ya gabata ne aka gano wata takarda da ta umarci shugabannin kananan hukumomin Kano 44 da su fitar da N670m domin gyara da sayen motocin Khalifa Muhammadu Sanusi II.

Sarki
Gwanatin Kano ta kare kanta kan sayawa Sarki sababbin motoci Hoto: King SLS The Legend/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnati, ta yi karin bayani a hirar da kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida na Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya ya yi wanda aka wallafa a shafin Facebook na Hikima rediyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamred Waiya ya bayyana cewa gyaran ababen hawa ko saya wa sarakuna sababbin motoci ba sabon al’amari ba ne, ko abin da ya saba ka'ida.

Gwamnati ta magantu kan gyaran motocin Sarki

Leadership News ta ruwaito Kwamred Waiya ya bayyana cewa sun yi mamakin yadda ake ta cece-kuce kan gyaran ababen hawan sarakuna, ganin cewa hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati ta yi musu hakan.

Ya kara da cewa:

“Hakki ne na sarki a kan gwamnatin jiha ta saya masa (abin hawa), ba kuma gwamnatin Kano ba ce ta fara hakan.
"Duka gwamnatoci, ka bincika baki daya, suna sayawa sarakuna motoci, suna ba wa hakimai abubuwan da suka shafi hakkinsu na albashi da wasu abubuwa irin wannan.”

Waiya ya kara da cewa daga cikin motocin da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ke hawa, ko a gwamnatance ba lallai a iya sayen su ba saboda tsadarsu.

Waiya
Kwamishinan yada labaran Kano, ya ce sayawa sarakuna motoci ba almubazzaranci ba ne Hoto: Ibrahim A. Waiya
Asali: Facebook

Ya shawarci jama’a da su rika yada labaran alheri da gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ke yi, maimakon kokarin yada abubuwan da ke kunshe da shakku.

'Ana sayawa sarakuna motoci a Kano,' Waiya

Kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida ya bayyana cewa gwamnatocin da suka gabata a Kano sun sayawa sarakuna sababbin motoci a zamaninsu.

Ya bayyana cewa yin hakan ba barnatar da dukiyar al’umma ba ne, domin kadan ne daga cikin abubuwan da ya dace a yi wa sarakuna.

Kwamred Waiya ya kara da cewa:

“Lokacin Mallam Ibrahim Shekarau yana gwamna, ya sai wa hakimai 44 sababbin Jeep Prado. A wancan lokacin, sai wanda ya isa ne ke hawa Prado Jeep.”
“Bayan wannan, lokacin mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da ya kirkiro masarautu na kwaryar wasa, ai ya sai wa dukkanin sarakunan motoci gaba daya.”

Waiya ya kara da cewa ba Sarki ake sayarwa motoci ba, masarauta ake sayawa motoci.

Gwamnatin Kano za ta saya wa Sanusi motoci

A baya, kun samu labarin cewa gwamnatin Kano ta amince da sayen sababbin motoci da kuma gyaran wasu tsofaffi ga masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.

Wannan mataki na gwamnatin Kano na zuwa ne makonni bayan dawo da Sanusi II a matsayin Sarki, inda gwamnatin ta fara daukar matakan farfaɗo da masarautar.

Gwamnati ta umarci kowace daga cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar da su fitar da Naira miliyan 15.2, wanda jimillar kuɗin baki daya ya kai Naira miliyan 670.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.