Majalisa Ta Karɓi Sunayen Shugabannin Sababbin Hukumomin da Tinubu Ya Kafa
- Shugaba Bola Tinubu ya aika da sunayen shugabannin sababbin hukumomin raya yankuna uku zuwa majalisar dattawa don tantancewa
- Tsohon Sanata Olubunmi Adetunbi, Cosmas Akiyir da Chibudom Nwuche su ne shugabanni da aka gabatar don jagorantar hukumomin
- Majalisar dattawa ta tura sunayen zuwa kwamitocin da suka dace domin tantancewa kafin amincewa da nadin a hukumance
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Majalisar Dattawa ta karɓi takardar buƙatar tabbatar da nadin mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya aika domin jagorantar Hukumomin Ci Gaban Arewa ta Tsakiya (NCDC), Kudu maso Yamma (SWDC), da Kudu maso Kudu (SSDC).
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar da Shugaba Tinubu ya aika masu yayin zaman majalisar ranar Alhamis.

Asali: Facebook
The Cable ta wallafa cewa an kafa wadannan hukumomi ne domin hanzarta ayyukan raya kasa da bunkasa tattalin arziki a shiyyoyin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dukkanin hukumomin za su gudanar da ayyukansu a ƙarƙashin kulawar dokoki daga majalisar tarayya.
Mutanen da Tinubu zai nada a hukumar SWDC
A cewar rahoton AIT, Shugaba Tinubu ya gabatar da sunayen mutum 18 da zai nada a Hukumar Raya Kudu maso Yamma (SWDC).
Rahoton ya ce tsohon Sanata daga jihar Ekiti, Olubunmi Adetunbi zai zama Shugaban Hukumar, yayin da Charles Akinola zai zama Manajan Darakta.

Asali: Facebook
Sauran sun hada da Bolaji Ariyo, Joseph Olugbenga, Scholastica Omoworare, Olumuyiwa Olabimtan, Adewinle Martins, Ibrahim Olaifa, Kabiru Lakwaya, da karin wasu.
Wadanda Tinubu zai nada a Arewa ta Tsakiya
A hukumar NCDC, Cosmas Akiyir ne zai zama Shugaban Hukumar, yayin da Tsenyil Yiltsen zai rike mukamin Manajan Darakta.
Sai Dauda Kigbu, Zakari Jikantoro, Suleiman Ali, Bunmi Olusona, Umar Mantu, Atotse Abraham, Solomon Adodo, Abdulkadir Usman, Habu Mamman, da Atinuke Owolabi.
Sauran sun hada da Rachel Nse, Boniface Izziogu, James Uloko, Princess Ajanah Bilgis Sani, Aishatu Ibrahim da Muhammad Bashar.
Sauran mutanen da za su samu mukamai
A hukumar SSDC, Shugaba Tinubu ya zabi Chibudom Nwuche a matsayin Shugaban Hukuma, yayin da Usoro Offiong Akpabio zai rike matsayin Manajan Darakta.
Bayan karanta takardar daga Shugaban kasa, Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio, ya mika sunayen zuwa ga kwamitocin da suka dace domin tantancewa da tabbatar da nadin su.
Ana sa ran majalisar za ta gudanar da tantancewa a makonni masu zuwa kafin a amince da sunayen a hukumance.
Tinubu ya nada sababbin shugabanni
A baya, mun wallafa cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya sanar da nada majalisar gudanarwa ta farko a sabuwar Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma (NWDC) domin samar da ci gaba.
Wannan naɗe-naɗe na zuwa ne biyo bayan amincewar Shugaba Tinubu da kudirin kafa hukumar NWDC a watan Yuli, wanda ake fatan zai taimaka wajen kara bunkasa ci gaban yankin.
Kafa majalisar gudanarwa wata babbar alama ce da ke nuna cewa hukumar za ta fara aiki da gaggawa domin magance matsalolin da ke addabar jihohin da ke shiyyar Arewa maso Gabas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng