Alwashin Sojojin Najeriya, Amurka kan Tsaro bayan Hare Hare Sun Karu a Kudu da Arewa

Alwashin Sojojin Najeriya, Amurka kan Tsaro bayan Hare Hare Sun Karu a Kudu da Arewa

  • Sojojin Najeriya da na Amurka sun yi magana kan hadakar da suke yi saboda yaki da ta'addanci a fadin kasar baki daya
  • Kasashen biyu sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa hadin gwiwa wajen yaki ta hanyar musayar bayanan sirri da horaswa
  • Hedikwatar Tsaro ta bayyana cewa dakarun kasashen biyu sun gudanar da hare-haren hadin gwiwa kan 'yan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sojojin Najeriya da Rundunar Sojin Amurka mai kula da Nahiyar Afirka (AFRICOM) sun yi magana kan yaki da ta'addanci.

Kasashen guda biyu sun tabbatar da kudurinsu na karfafa hadin gwiwar tsaro domin fatattakar 'yan ta'adda.

Sojojin Najeriya da na Amurka sun haɗa kai kan rashin tsaro
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da Donald Trump na Amurka. Hoto: Bayo Onanuga, Donald J Trump.
Source: Twitter

An sake jaddada wannan kuduri ne yayin wata tattaunawa da Premium Times ta sanya ido a kanta a ranar Talata 9 ga watan Yunin 2026.

Musabbabin haɗin gwiwar Najeriya da Amurka

Kara karanta wannan

Rai bakon duniya: Shugaban Izala a Kebbi ya rasa ransa a hannun 'yan bindiga

Sun ce musayar bayanan sirri, gudanar da ayyukan hadin gwiwa da horas da jami'ai su ne ginshikan wannan kawance.

An kulla wannan hadin gwiwa ne bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.

Da take amsa tambaya kan tsawon lokacin hadin gwiwar, Daraktar Hulda da Jama'a ta AFRICOM, Kanal Rebecca Heyse, ta ce hadin kan kasashen biyu ya ginu ne bisa mutunta ikon Najeriya da bukatun bai daya.

Ta ce:

"Ayyukanmu da Najeriya suna gudana ne cikin cikakken mutunta ikon kasar. Muna aiki ne bisa gayyata kuma karkashin tsarin US-Nigeria Joint Working Group.
"Muddin akwai barazanar tsaro ta bai daya kuma tsarin yana da amfani ga bangarorin biyu, Amurka za ta ci gaba da kasancewa cikin wannan hadin gwiwa."

A cewarta, Amurka za ta ci gaba da taimaka wa Najeriya muddin kasashen biyu suna ganin hadin gwiwar na da amfani wajen tunkarar barazanar tsaro da suke fuskanta tare.

Sai dai Kanal Heyse ta kauce wa amsa tambayoyi kan matsayin Gwamnatin Amurka game da zargin kisan kiyashi kan Kiristoci.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka yi wa 'yan Boko Haram dabara wajen ceto mutane 360 da aka sace a Borno

Ana samun nasara a gadin guiwar Najeriya da Amurka
Ministan tsaro, Christopher Musa. Hoto: Gen GC Musa.
Source: Twitter

Yadda Najeriya ta buƙaci taimakon Amurka

Mai magana da yawun Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce irin taimakon da Amurka za ta ci gaba da bayarwa zai dogara ne da irin bukatun ayyukan tsaron Najeriya.

Ya ce:

"Wannan hadin gwiwa tana gudana ne bisa bukatar Najeriya. Kwarewa da fasahohin musamman da Amurka ke kawowa abubuwa ne da muke bukata, kuma muddin muna bukatarsu za mu ci gaba da aiki tare."

Yayin tattaunawar, Janar Uba ya bayyana cewa hadin gwiwar ya zarce musayar bayanan sirri da horaswa zuwa gudanar da ayyukan hadin gwiwa kai tsaye kan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Lokacin da aka tura sojojin Amurka a farkon shekarar nan, jami'in ya ce ba za su shiga fagen daga kai tsaye ba, illa samar da tallafin fasaha da horaswa, cewar Punch.

Harin Amurka ya hallaka ƴan ta'adda a Borno

A wani labarin, an ji cewa sojojin Amurka sun kara ba da gudummuwa wajen kai farmakin sama kan sansanin kungiyar 'yan ta'adda ISWAP a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Sojoji da dama sun mutu da 'yan ta'adda suka bude wuta ana ruwan sama a Borno

Rahoto ya nuna cewa harin ya yi sanadiyyar hallaka mayakan kungiyar ISWAP 21 a yankin Arege da ke karamar hukumar Kukawa.

Majiyar ta kara da cewa wannan farmakin wani bangare ne na ci gaba da hadin gwiwar da ke tsakanin Najeriya da Amurka wajen yaki da ta’addanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.