Mele Kyari Ya Yi Magana kan Bincikensa, Ya Bayyana Shirin da Yake Yi
- Tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya bayyana cewa ya gudanar da shugabancinsa bisa tsoron Allah
- Mele Kyari ya bayyana cewa a.shirye yake ya ba da bayani kan yadda ya gudanar da shugabancin kamfanin na NNPCL
- Tsohon shugaban na NNPCL ya nuna godiyarsa ga Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu kan damar da suka ba shi ta shugabantar kamfanin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ya yi magana kan batun bincikensa da ake yi.
Mele Kyari ya bayyana cewa ya gudanar da aikinsa na shugabantar kamfanin NNPCL da tsoron Allah.

Asali: Facebook
Mele Kyari ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana ta maganganu kan shugabancin Mele Kyari
Tun bayan babban sauyin da aka yi a kamfanin NNPCL, rahotanni da dama sun bayyana dangane da lokacin aikinsa a matsayin shugaba.
A cewar wani rahoto, an gano Naira biliyan 80 a asusun ɗaya daga cikin tsofaffin daraktocin matatar mai da aka sallama, wanda ya yi aiki a ƙarƙashin jagorancin Mele Kyari.
Bayo Ojulari, wanda ya gaji Mele Kyari, ya fara wani babban sauyi wanda ya kai ga korar mutane da dama da suka yi aiki ƙarƙashin tsohon shugaban kamfanin na NNPCL.
Haka kuma, rahotanni daban-daban sun fito dangane da zargin cin hanci da rashawa a lokacin mulkinsa.
Me Mele Kyari ya ce kan bincikensa a NNPCL
Mele Kyari ya ce ya yi wa Najeriya aiki da tsoron Allah kuma a shirye yake ya bayyana yadda ya gudanar da aikinsa.

Asali: Facebook
“A cikin ƴan kwanakin nan, musamman cikin sa’o’i biyu da suka gabata, na ci karo da kira daga ƴan uwa da abokai masu nuna damuwa dangane da wani labarin da wata jaridar yanar gizo ta fitar cewa ina hannun EFCC."
“Wannan ƙarairayi ne da wata maƙarƙashiya da aka tsara domin cimma wata manufa da kawai waɗanda suka ɗauki nauyin labarin suka sani.”
“A halin yanzu, ina hutawa bayan an rusa shugabanci da kwamitin gudanarwa na NNPCL, wanda na kasance shugaba."
“Ya kamata a fahimci cewa, bayan na yi aiki a NNPC sannan daga baya NNPCL na tsawon shekaru 34, ciki har da shekaru 17 a muƙaman gudanarwa, kuma musamman shekara biyar da watanni tara da suka gabata, ban samu lokacin hutu ba, ko da na makonni biyu."
“Don haka, ina godiya ga damar da na samu na yin aiki a ƙarƙashin masu girma Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu."
“Dole ne na jaddada cewa na yi aiki da tsoron Allah, da sanin cewa, a matsayina na Musulmi, ko da ba zan ba da bayani a gaban mutane ba, lallai zan ba da bayani a gaban Allah."
“Na fi so na bayar da bayani a gaban hukumomin ɗan Adam. Don haka, bayan na yi aiki a matsayin jami’in gwamnati, a shirye na ke kuma ina farin ciki na bayar da bayani kan yadda na gudanar da aikina a wannan duniya."
- Mele Kyari
Ƙungoya ta buƙaci a binciki Mele Kyari
A wani labarin kuma, kun ji cewa an buƙaci gwamnatin tarayya ta binciki tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari.
Ƙungiyar CCA ta gudannar da zanga-zanga a gaban ofishin minista shari'a, Lateef Fagbemi domin ganin an binciki tsohon shugaban kamfanin na NNPCL.
Shugaban ƙungiyar, Kabir Matazu, ya bukaci Lateef Fagbemi da ya binciki duk wasu harkokin NNPCL ƙarƙashin jagorancin Mele Kyari cikin shekaru biyar da suka wuce.
Asali: Legit.ng