Trump Ya Ce zai Kyale Iran Ta Ba Isra'ila Wuta idan Netanyahu Ya Tsokano Fada
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya gargadi Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kan hare-haren da suka kai wa juna da Iran
- A gargadin da ya yi, shugaba Trump ya nuna cewa ba zai taya Netanyahu yaki da Iran ba idan babban rikici ya sake barkewa a tsakaninsu
- Tun da farko Trump ya nuna damuwa kan hare-haren, inda ya bukaci Isra'ila da Iran su koma teburin tattaunawa maimakon yaki da juna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka, Donald Trump ya kara janye jiki daga taimakawa Isra'ila a takaddamar da ake a Gabas ta Tsakiya.
Yayin da Benjamin Netanyahu ya yi magana da Trump ta wayar tarho, shugaban Amurka ya yi gargadin ba zai taya Isra'ila yaki da Iran ba.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa gargaɗin Trump ya zo ne yayin da Isra’ila da Iran suka dakatar da hare-hare kuma ake ci gaba da tattaunawar da ba ta kai tsaye ba domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
Iran: Gargadin Trump ga Isra'ila
Shugaban Amurka Donald Trump ya gargaɗi Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu cewa zai iya tsinci kansa yana yaƙi shi kaɗai idan Isra’ila ta koma yaƙi da Iran.
Gargaɗin da ya yi a ranar Litinin ya zo ne yayin da Isra’ila da Iran suka ce za su dakatar da hare-hare bayan mafi girman tashin hankali da aka samu tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Afrilun 2026.
Trump, wanda rahotanni suka ce yana ƙara nuna rashin jin daɗi da Netanyahu, ya buƙaci ɓangarorin biyu su daina yaki a wani saƙo da ya fitar, yana mai cewa za a cigaba da tattaunawa.
Abin da Trump ya cewa Netanyahu
A wani rahoto da Reuters ya fitar, Trump ya ce ya gargaɗi Netanyahu kan abin da zai biyo baya idan ya cigaba da yaki da Iran.
“Na ce masa, ‘Bibi, ka yi hankali, domin nan ba da jimawa ba za ka kasance kai kaɗai,’”
In ji Trump.
Yadda sabon rikicin ya fara
Sabon tashin hankalin ya fara ne a ranar Lahadi bayan harin bam mai muni da Isra’ila ta kai wa Beirut, babban birnin Lebanon.
Iran, wadda ta daɗe tana cewa yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta dogara ne kan kawo ƙarshen faɗa a Lebanon, ta mayar da martani da harba makamai masu linzami zuwa Arewacin Isra’ila.

Source: Getty Images
Rahotanni sun ce Trump ya kira Netanyahu a yammacin Lahadi ya roƙe shi da kada ya mayar da martani, amma Isra’ila ta kai hare-hare kan Iran da sanyin safiyar Litinin.
Isra'ila ta kai hari Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun Isra’ila sun kai hari kan tsarin kariyar sararin samaniyar Iran da kuma wata masana’antar sarrafa sinadarai.
Bayan harin, kasar Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan irin wannan masana’anta a Haifa tare da kai hari kan sansanonin sojin saman Isra’ila guda biyu.
Duk da hare-haren da kasashen suka kai wa juna a ranar Litinin, ba a bayar da rahoton mutuwar kowa ba daga ɓangarorin biyu ba zuwa yanzu.
Asali: Legit.ng

