Ba EFCC Ke Tsare da Ni Ba: Mele Kyari Ya Karyata Jita-Jitar EFCC Ta Yi Masa Kamun Kazar Kuku

Ba EFCC Ke Tsare da Ni Ba: Mele Kyari Ya Karyata Jita-Jitar EFCC Ta Yi Masa Kamun Kazar Kuku

  • Tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari, ya musanta labarin da ke cewa EFCC ta kama shi ta kuma tsare shi kwanan nan
  • Ya bayyana cewa yana hutu ne bayan saukarsa daga mukami, kuma a shirye yake ya amsa kowace tambaya ta doka
  • Kyari ya yi kira ga 'yan jarida da su daina yada jita-jita da ke iya illata sunan mutum da martabar kasa

Najeriya - Tsohon Shugaban Rukunin Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya fito karara ya karyata rahoton da ya yadu a kafafen sada zumunta da ke cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kama shi.

Kyari ya bayyana cewa labarin karya ne kawai da nufin bata masa suna da kuma rage karfin tasirinsa a idon al’umma. Ya ce yanzu haka yana cikin hutun da ya cancanta bayan an sauke shi daga mukaminsa.

A cewar Kyari, ya shafe shekaru 34 yana aiki da NNPCL, inda kusan shekaru shida daga cikinsu ya yi a matsayin babban darakta kuma shugaban kamfanin.

Kyari ya karyata batun kama shi
Kyari ya karyata batun shiga hannun EFCC | Hoto: Mele Kyari, OFR
Asali: Facebook

Na yi aiki tsakani na da Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya yi aikinsa cikin tsoron Allah da gaskiya, yana mai cewa bai da wata damuwa da tambayoyi daga kowace hukuma.

A cewarsa cikin wata wallafar da ya yi a shafinsa na X:

"Na yi aiki da tsoron Allah. Na san cewa ko da ban bada bahasi a gaban mutane ba, to zan bada bahasi a gaban Allah. Ina da kwarin gwiwar cewa duk abin da na yi yana cikin gaskiya da rikon amana."

Kyari ya ce kiraye-kirayen da ya samu daga ‘yan uwa da abokai cikin ‘yan sa’o’i kadan da suka gabata sun saka shi a damuwa, inda ya tabbatar musu da cewa yana cikin kwanciyar hankali a gida yana hutawa a gida.

Wannan bata sunan Najeriya ne

Ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda wasu kafafen labarai ke yada labaran karya ba tare da tantance gaskiya ba.

Ya ce irin wannan abu yana iya janyo matsala ga ci gaban kasa, musamman idan aka yi la’akari da yadda ‘yan kasuwa da masu zuba jari daga kasashen waje ke kallon Najeriya.

Ya kara da cewa:

“Irin wadannan jita-jita da aka kirkira ba su amfani ga kasa ko kamfanoni kamar NNPCL. Suna iya sanya kasashen waje su dauka cewa ba zaman lafiya ko gaskiya a Najeriya.”

Yadda aka dakatar da Kyari

A ranar 2 ga Afrilu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauke Kyari daga mukaminsa na GMD na kamfanin NNPCL tare da tsohon shugaban hukumar, Pius Akinyelure.

A madadinsu, Tinubu ya nada Bashir Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin.

Kyari ya godewa dangi da abokai da suka nuna damuwa, yana mai jaddada cewa a shirye yake ya amsa duk wata tambaya ta doka game da lokacin da ya kwashe yana shugabantar NNPCL.

Kadan daga tarihin Kyari

Shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Malam Mele Kyari ya ba da labarin yadda ya taso daga almajiranci zuwa matakin da yake a yanzu.

Mele Kyari ya bayyana cewa ya tashi daga makarantar Almajirai wacce aka fi sani da Tsangaya har ya zama shugaban kamfanin mai na kasa watau NNPCL

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: