An Gwabza Fada tsakanin Dakarun Sojoji da Ƴan Sanda, An Ga Abin da Ya Faru a Bidiyo
- Rikici ya barke tsakanin ’yan sanda da sojojin sama a Jeddo, jihar Delta, yayin da aka kama wani mutum dauke da miyagun kwayoyi
- Sojojin sama sun bukaci a saki wanda ake zargi, amma ’yan sanda suka ki, lamarin ya jawo arangama tsakanin jami’an tsaron
- Kakakin ’yan sandan jihar Delta ya ce an fara bincike kan lamarin, tare da tabbatar da cewa hakan ba zai sake faruwa ba a nan gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Delta - Fada ya barke tsakanin ’yan sanda da sojojin sama a shingen bincike da ke Jeddo, jihar Delta, wanda ya dauki hankalin jama’a.
Kakakin rundunar ’yan sanda na Delta, SP Edafe Bright, ya ce rikicin ya faru ne yayin da ’yan sanda ke rakiyar wani mai safarar miyagun kwayoyi.

Asali: Twitter
Sojoji da 'yan sanda sun kaure da fada
A sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, SP Edafe ya ce an kama wanda ake zargin da kodin, tabar wiwi, inda aka yi kokarin kai shi ofishin ’yan sanda, lokacin da abin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce lokacin da 'yan sandan suka isa shingen binciken, sojojin saman da ake zargin sun san wanda aka kama, suka tare ayarin, tare da neman a sake shi.
SP Edafe ya bayyana cewa sojojin saman sun bukaci sakin wanda ake zargi, amma ’yan sandan suka ki, lamarin da ya jawo suka ba hammata iska nan take.
An dauki matakin magance rikicin
Sanarwar kakakin 'yan sandan ta ce:
"Jami’an QRS sun kama wani mutumi dauke da miyagun kwayoyi, amma sojojin sama sun tare su, ana neman sakin wanda ake zargin."
Edafe ya ce wannan rikicin abin takaici ne, amma hukumomin da abin ya shafa sun dauki mataki don ganin hakan ba ya sake faruwa.
Ya kara da cewa:
"Ana bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa dangantaka mai kyau da ke tsakanin sojojin sama da ’yan sanda ba ta lalace ba."
An yi kira ga mazauna Delta
Kakakin ya tabbatar da cewa kwamishinan ’yan sanda, CP Olufemi Abaniwonda, da shugabannin rundunar sojan sama suna aiki tare kan magance matsalar.
An bayyana cewa za a sanya sabbin tsare-tsare don kare irin wannan abin kunya daga sake faruwa a jihar Delta.
Hukumar ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Kalli bidiyon rigimar, wanda Punch ta wallafa a kasa:
Fadan sojoji da 'yan sanda ya yi ajalin mutum
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani dan sanda mai suna Jacob Daniel ya rasa ransa a wata arangama tsakanin sojoji da ’yan sanda a jihar Adamawa.
Lamarin ya faru ne bayan kisan wani soja, Sajan Ibrahim Ali, wanda dan sanda ya kashe a shekarar 2022, abin da ya kara tayar da hankali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng