Mutanen Gari Sun Hadu, Sun Kutsa Daji, Sun Yi wa 'Yan Bindiga Jina Jina har Suka Mutu

Mutanen Gari Sun Hadu, Sun Kutsa Daji, Sun Yi wa 'Yan Bindiga Jina Jina har Suka Mutu

  • Wasu matasa sun hallaka mutum uku da ake zargi da garkuwa da mutane a jihar Delta bayan sun sace wani mafarauci
  • Rahotanni sun nuna an bi sawun masu garkuwa da mutanen ne bayan sun kira iyalan wanda suka sace don neman kudin fansa
  • ‘Yan sanda sun bazama a yankin don tabbatar da tsaro, amma har yanzu ba a kama kowa ba dangane da kisan da aka yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Wasu fusatattun matasa sun hallaka mutum uku da ake zargi da aikata garkuwa da mutane a Ozanogogo, yankin Ika South na Jihar Delta.

Rahotanni sun nuna cewa wadanda ake zargin sun sace wani mafarauci mai suna Oza Smart, wanda hakan ya haifar da tashin hankali a yankin.

Kara karanta wannan

An yi jina jina da 'yan banga suka gwabza kazamin fada da 'yan bindiga

Yan bindiga
Mutanen gari sun kashe 'yan bindiga a Delta. Hoto: Dave Clark
Asali: Getty Images

Rahoton Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, lokacin da masu garkuwar suka kira matarsa don neman kudin fansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka cafke masu garkuwa a Delta

Bayan samun labarin sace Oza Smart, matasan yankin Ozanogogo sun taru suka bi sawu domin gano inda masu garkuwar suka buya.

A cewar wata majiya, an gano su ne ta hanyar bin diddigin kiran wayar da suka yi ga iyalan wanda suka sace domin neman kudin fansa.

Bayan samun sahihan bayanai, matasan yankin sun kutsa cikin daji inda suka yi wa masu garkuwar kwanton bauna.

A cikin fafatawar da aka yi, matasan sun samu nasarar kubutar da wanda aka sace tare da cafke uku daga cikin masu garkuwar, yayin da sauran biyu suka tsere.

Matasa sun hallaka wadanda ake zargi

Kara karanta wannan

Masu garkuwa sun yi amfani da jirgin sama wajen satar mutum a Kano

Bayan matasan sun kama wadanda ake zargi, ba su bata lokaci ba suka fara dukansu da sanduna, duwatsu da wasu makamai.

Matasan sun fusata ne saboda yadda garkuwa da mutane ke karuwa a yankin, suna ganin cewa hukuma ba ta daukar matakin da ya dace.

Duk da kokarin da ‘yan sanda suka yi na hana matasan kona wadanda ake zargi da garkuwa, sun riga sun raunata su matuka, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsu.

An kai wadanda suka jikkata asibiti

A daidai lokacin da lamarin ke faruwa, DPO na 'yan sanda, DSP Jafaru Umaru, ya samu labari, inda ya hanzarta tura tawagar ‘yan sanda zuwa wurin.

Da isarsu, sun tarar da gawarwakin wadanda ake zargi, yayin da suka dauki wanda aka kubutar suka kai shi asibiti don duba lafiyarsa.

Bayan haka, ‘yan sanda sun dauki gawarwakin wadanda aka kashe suka kai su asibitin Agbor domin gudanar da bincike da kuma ajiyar gawarwakin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan masu taron siyasa a Najeriya, an harbi mutane 14

Kayode
Sufeton 'yan sandan Najeriya. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An dauki matakan tsaro a yankin

Bayan aukuwar lamarin, rundunar ‘yan sanda ta fara bincike domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma gano wadanda suka aikata kisan.

Duk da haka, har yanzu ba a kama kowa ba dangane da kisan wadanda ake zargin da garkuwa da mutane.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin ya ce an dauki matakan tsaro domin hana aukuwar irin wannan lamari a gaba, tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

An kama masu garkuwa a jihar Legas

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta kama wasu mutane 'yan kasar waje da suka yi garkuwa da wani mutum a Legas.

Rahotanni sun nuna cewa wadanda ake zargi da garkuwar sun dauko mutumin ne a jirgi daga Kano zuwa Legas inda suka bukaci kudin fansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng