Laraba: Rana za Ta Yi Zafi sosai a Arewa, za a Samu Ruwan Sama a Neja da Jihohi 7

Laraba: Rana za Ta Yi Zafi sosai a Arewa, za a Samu Ruwan Sama a Neja da Jihohi 7

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a fuskanci yanayi mabanbanta tun daga rana mai zafi zuwa ruwan sama mai hade da tsawa a ranar Laraba
  • Yayin da jihohin Arewa maso Gabas biyu za su samun ruwan sama, ana sa ran ruwan zai sauka a jihohi shida na Arewa ta Tsakiya, ciki har da Filato
  • Hukumar ta ja kunnen jama'a da su kiyaye walƙiya da kuma ambaliyar ruwa a wasu yankuna, yayin da direbobi ke buƙatar yin taka-tsantsan.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026.

Rahoton ya nuna cewa wasu jihohi za su fuskanci ruwan sama mai yawa har ma hade da tsawa, yayin da wasu za su fuskanci zafin rana sosai.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗauki mataki kan buƙatar belin El Rufai, Malam zai zauna a hannun ICPC

NiMet ta yi hasashen cewa za a samu saukar ruwan a wasu jihohin Arewa
Ruwan sama na sauka a wani yanki na Najeriya. Hoto: Sani Hamza / Staff.
Source: Original

Hukumar NiMet ta fitar da rahoton hasashen yanayin ne a shafinta na X a yammacin Talata, 21 ga Afrilu, 2021, domin bai wa jama'a damar kasancewa cikin shiri.

Hasashen yanayi a wasu jihohin Arewa

Da safiyar Laraba, ana sa ran za a samu hasken rana a daukacin yankunan arewacin ƙasar. Sai dai, ranar za ta yi zafi sosai, inda NiMet ta nemi jama'a su rika yawaita shan ruwa a irin wannan lokaci.

Da yamma zuwa dare kuwa, hasashen NiMet ya nuna cewa za a samu ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi tare da tsawa a sassan jihohin Adamawa da Taraba.

Za a samu iska mai ƙarfi da walƙiya a wasu wuraren, wanda hakan ka iya haifar da tashin ƙura kafin ruwan ya fara sauka.

Hasashen yanayi a Filato, Neja

Idan muka leka a jihohin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran hadari zai hadu, amma rana za ta huto, a wasu sassan shiyyar. Za a samu yanayi mai ɗumi tun da safe har zuwa yamma.

Kara karanta wannan

Bayan sauya shekar Kwankwaso, wasu manyan jiga jigan siyasar Najeriya za su koma ADC

Da yamma zuwa dare, ana sa ran ruwan sama da tsawa za su sauka a sassan babban birnin tarayya (FCT), jihohin Nasarawa, Benue, Kogi, Neja, Plateau, da Kwara.

NiMet ta bukaci mutanen da ke a wadannan jihohi su tsara harkokinsu na waje da wuri kafin isowar hadarin.

Hasashen yanayi a jihohin Kudu

Da safiyar Laraba, ana sa ran hadari zai lullube sararin samaniya a daukacin yankin kudancin Najeriya tun daga safiya, tare da yiwuwar samun yyafi a wasu sassan.

Da yamma zuwa dare, ana sa ran ruwan sama mai ƙarfi da tsawa za su mamaye jihohin Imo, Abia, Anambra, Enugu, Ebonyi, Ondo, Ogun, Osun, Ekiti, Oyo, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River, Lagos, da Akwa Ibom.

NiMet ta ce za a sheka ruwan sama a wasu jihohin Najeriya.
Yara na wasa yayin da ake ruwa a garin Nafada, jihar Gombe. Hoto: Jamsy El-nfaty
Source: Facebook

Shawarwari da gargadi daga NiMet

Hukumar ta shawarci jama’a da su hattara da iska mai ƙarfi da ka iya dauka ko kayar da abubuwa, sannan a guji wuraren da ambaliyar ruwa ta saba shafa.

Hakanan, an shawarci direbobi da su yi tuƙi cikin natsuwa saboda rashin ganin gaba da kuma santsin hanya, tare da neman mafaka a gine-gine domin guje wa saukar walƙiya.

Kara karanta wannan

Neja da jihohin Arewa 10 za su fuskanci iska mai ƙarfi da ruwan sama gobe Juma'a

Hukumar ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da su rinka samun rahotannin yanayi na filayen jiragen sama daga NiMet kafin tashi ko sauka don tabbatar da aminci.

Karanta rahoton NiMet a nan kasa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com