Rigima ya kaure a JUTH kan amfani da hijabi da ma’akata da dalibai mata ke yi

Rigima ya kaure a JUTH kan amfani da hijabi da ma’akata da dalibai mata ke yi

- Ana kan tafka muhawara a asibitin koyarwa na jami’ar Jos kan yin amfani da hijabi

- Anyi zargin cewa an tursasa dalibai mata da ke karantar bangaren jinya Musulmai cire hijabansu

- Hukumar dake kula da asibitin, har ila yau, tace zarge-zargen duk kagaggen labari ne da aka shirya bata ma asibitin suna tare da haddasa rigingimun addini

Ana tafka gumurzu a asibitin koyarwa na jami’ar Jos yayin da dalibai mata musulmai masu daukar horo a asibitin suka yi zargin cewa ana tursasa su cire hijabi a sashin kiwon lafiya dake asibitin.

Fusatattun daliban sun bayyana ma jaridar Daily Trust cewa shugaban sashin kiwon lafiya na ci musu mutunci, inda suka yi zargin cewa ya basu zabin ko su bar makarantar, ko kuma su bar sumansu a bude.

A halin yanzu, kungiyar Coalition of Jos Concerned Youth Associations ta shiga lamarin.

Rigima ya kaure a JUTH kan amfani da hijabi da ma’akata da dalibai mata ke yi
Rigima ya kaure a JUTH kan amfani da hijabi da ma’akata da dalibai mata ke yi
Asali: Facebook

A wata wasika daga shugaban kungiyanr, Buhari Ibrahim Na Shehu zuwa ga babban darektan JUTH, Farfesa Edmund Banwat, kungiyar tace matakin da sashin kiwon lafiyan ta dauka ya kasance cin zarafi akan hakkokin dalibai musulmai mata.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun hallaka yan sa kai 5 a jihar Katsina

Na Shehu yace wannan yana daga cikin ya saba ma dokar kungiyar ma’aikatan jinya na kasa wanda ya baiwa dalibai musulmai da kiritoci damar sanya mayafai kamar yanda addinansu suka tanada.

Haka zalika, asibitin , a wani wasikar da ta aika ma jaridar Daily Trust a ranar 21 ga watan Mayu, ta bayyana zargin a matsayin karya.

Wasikan, wanda Bridget Omini ta sa hannu a madadin shugabancin asibitin, tace rahotanni dake cewa JUTH na razana dalibai musulmai mata da kora ba gaskiya bane illa kage mai manufar bata ma asibitin suna da kuma haddasa rikicin addinai.

Wasikar ta bayyana cewa sanya hijabi masu tsayi ya kasance hatsari ga dalibai da marasa lafiya a wajen yada cututtuka, an yarda da gajejjerun hijabi a asibitin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel