Zaben 11 Ga Watan Nuwamba: Jerin Gwamnonin Jihar Bayelsa Daga 1999 Zuwa Yanzu

Zaben 11 Ga Watan Nuwamba: Jerin Gwamnonin Jihar Bayelsa Daga 1999 Zuwa Yanzu

  • Ba boyayyen abu ba ne, yadda tsoffin gwamnonin jihar Bayelsa, suka ba da gudunmawa sosai wajen ci gaban jihar
  • Tun bayan da aka kafa Jihar Bayelsa, ta samu shugabanci daga zababbun gwamnonin dimokuradiyya guda biyar
  • Daga daga cikin gwamnonin kuwa, Goodluck Jonathan, ya samu nasarar zama mataimakin shugaban kasa, daga bisani ya zama shugaban kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Bayelsa - Jihar Bayelsa, jiha ce da ke a bakin teku, a Kudancin Najeriya, kuma tana a cikin yankin Neja Delta.

An ƙirƙiri jihar ne a shekarar 1996, kuma tana daya daga cikin jihohin da aka samar da su a baya-bayan nan, amma duk da haka, tana da dimbin kyawawan al'adu da na tarihi.

Kara karanta wannan

"Allah ya ba ku ikon sauke nauyi", Tinubu ya taya Diri, Ododo, Uzodimma murna

Gwamnonin jihar Bayelsa
Diepreye Alamieyeseigha ya zama zababben gwamnan jihar Bayelsa na farko ta hanyar zaben dimokradiyya. Hoto: New York Times/Henry Seriake Dickson/Oli Scarff
Asali: UGC

Jihar tana da manyan hanyoyin sadarwa na gabobin tekuna, manyan bishiyoyi, da rafuffuka, wanda hakan ya sa ta zama jiha mai ban sha'awa amma mai cike da kalubale.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yenagoa, babban birnin jihar, ta kasance cibiyar siyasa da tattalin arzikin jihar, yayin da 'yan kabilar Ijaw, masu al'adu da dabi'u na ban mamaki, suka zama kabila mafi rinjaye a Bayelsa.

Tattalin arzikin jihar ya ta'allaka ne a kan noma, kamun kifi, da bunkasar masana'antar mai da iskar gas, wanda ke ba da gudummawa ga yanayin tattalin arzikin Najeriya gaba daya.

A wannan labarin, za mu zayyana gwamnonin jihar Bayelsa tun daga 1999 zuwa yau.

Diepreye Alamieyeseigha (1999 - 2005)

Diepreye Alamieyeseigha, dan jam’iyyar PDP ne, shi ne gwamnan farar hula na farko a jihar Bayelsa, daga 1999 zuwa 2005.

Gwamnatin Alamieyeseigha, ta fuskanci kalubale da dama, da suka hada da zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma karkatar da kudade, wanda a karshe ya kai ga tsige shi a shekara ta 2005.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun kori masu zabe a Bayelsa, sun yi harbe-harbe

Al’amarin Alamieyeseigha ya zama kanun labarin manyan jaridu bayan da ya yi kaurin suna wajen wasan buya da hukumar shige da fice ta kasar Birtaniya, inda ya ke yin shigar mata duk lokacin da zai shiga ko zai fita daga kasar.

Goodluck Jonathan (2005 - 2007)

Bayan tsige Alamieyeseigha mataimakinsa Goodluck Jonathan ya hau kujerar gwamnan jihar Bayelsa.

Daga baya ya zama mataimakin shugaban kasar Najeriya, kuma a shekarar 2010, shugaban kasar Najeriya na lokacin, Umaru 'Yar'aduwa ya rasu, inda Jonathan ya maye gurbinsa a shugabancin kasar.

Timipre Sylva (2007 - 2012)

Timipre Sylva, wanda shi ma dan PDP ne, an zabe shi matsayin gwamna jihar Bayelsa a shekarar 2007.

Ya yi mulki har na wa'adi biyu daga 2007 zuwa 2012, amma dalili ya yi dalili aka tsige shi a wa’adi na biyu na mulkinsa.

An yi wa gwamnatin Sylva tambari da gwamnati mai tsattsauran ra'ayi, amma wacce ta shimfida ayyuka, kuma shi ne gwamna na farko a jihar Bayelsa da aka sake zabar shi a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Imo 2023: 'Yan sanda sun yi arangama da wakilan jam’iyya, an yi harbe-harbe

Seriake Dickson (2012 - 2020)

Seriake Dickson, wanda kuma dan jam’iyyar PDP ne, ya hau kujerar gwamna a shekarar 2012 kuma an sake zabensa a karo na biyu a shekarar 2016.

A zamanin mulkinsa, a mayar da hankali ne kan ayyukan raya kasa da samar da ababen more rayuwa, kamar su ilimi, da kiwon lafiya, da dai sauransu.

Douye Diri (2020 - zuwa yanzu)

Douye Diri, dan jam’iyyar PDP ya zama gwamnan jihar Bayelsa a watan Fabrairun 2020 bayan da kotun kolin Najeriya ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Ya gaji Seriake Dickson, kuma ya yi ayyuka masu yawa na ci gaban jihar, tun hawansa mulki.

Diri na neman tazarce a zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Douye Diri ya samu tazarce

Legit Hausa ta ruwaito maku cewa hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya (INEC) ta ayyana Duoye Diri na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun damke wasu motoci 3 da ake zargi a zaben jihar Kogi

Diri, wanda ya yi takara don neman zarcewa karo na biyu a ofis, ya samu kuri'u 175,196 inda ya kada babban abokin hamyarsa, Timipre Sylva na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u 110,108 kamar yadda Legit Hausa ta tattaro daga Channels Television.

Jerin 'yan takarar gwamna a jihar Bayelsa

A wani labarin, kunji yan takara da jam'iyyun siyasa 15 ne za su fafata da Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Bayelsa da za a gudanar a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel